'Yan Bindiga Sun Kashe DPO Da Jami'ansa A Jihar Neja

'Yan Bindiga Sun Kashe DPO Da Jami'ansa A Jihar Neja

Daga Abbakar Aleeyu Anache.

Yan bindiga a Najeriya sun katse hanyar Minna zuwa Abuja inda suka kashe baturen 'yan sanda da ake kira DPO Mukhtar Sabiu tare da wasu jami'ansa guda 4,

Rahotanni daga yankin sun ce an yi arangama ne tsakanin jami'an tsaro da tawagar yan bindigar a kusa da kauyen kwakuti da ke kan hanyar Minna zuwa Suleja abin da ya kai ga rasa rayukan zaratan yan sandan Najeriya,

Kakakin rundunar yan sandan jihar Neja Wasiu Abiodun ya tabbatar da mutuwar DPO da jami'ansa guda 4 lokacin da suka yi musayar wuta da tawagar barayin,

Sanawar da Abiodun ya bayar ta ce yayin fafatawar da aka yi tsakanin tawagar jami'an tsaron da ta hada da sojoji da yan sanda da kuma yan sa-kai an hallaka yan bindigar da dama yayin da wasu kuma suka samu raunuka.