Dan Kwallon Nijeriya, Abdullahi Shehu Ya Dauki Nauyin Kudin Jinyar Wani Mara Lafiya A Sokoto

Dan Kwallon Nijeriya, Abdullahi Shehu Ya Dauki Nauyin Kudin Jinyar Wani Mara Lafiya A Sokoto
Dan Kwallon Nijeriya, Abdullahi Shehu Ya Dauki Nauyin Kudin Jinyar Wani Mara Lafiya A Sokoto
Dan kwallon kafar wanda ke taka ledarsa a kungiyar Bursaspor dake kasar Turkiya, ya yi wannan abin alheri ne a lokacin da ya ga ana nemawa wannan bawan Allah taimako a kafafen sadarwa na zamani, inda take ya nemi sanin ko nawa ne za a yi masa tiyata, wanda tuni aka ba shi bayanin cewa naira dubu sittin ne (60,000) za a yi masa tiyatar, cikin tsananin tausayi ya bada umurnin ba shi kudin domin a je a yi masa aikin. 
Wannan ba karamin abu bane, kuma ceton rai, muna rokon Allah ya kara taimakonsa kamar yadda ya taimaki wannan bawan Allah mai suna Malam Sanusi wanda ke zaune a Diploma cikin birnin jihar sokoto. 
Allah ya saka masa da gidan Aljanna, ya daukaka darajarsa, amin.