Ambaliyar Ruwa a Yobe: Hukumar SEMA ta tallafa wa magidanta sama 1000 a Nguru

Ambaliyar Ruwa a Yobe: Hukumar SEMA ta tallafa wa magidanta sama 1000 a Nguru

Daga Muhammad Maitela, Damaturu.

Biyo bayan ibtila'in ambaliyar ruwan da ya jefa yankuna da dama a jihar Yobe cikin mawuyacin hali, Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa a jihar Yobe (SEMA) ta tallafa wa sama da magidanta 1000 da kayan abinci a karamar hukumar Nguru da ke jihar, domin saukaka halin kuncin da ambaliyar ruwan ta jawo a yankin.

Da yake jagorantar raba kayan tallafin, shugaban Hukumar, Dr. Mohammed Goje ya ce ya SEMA ta yi nasarar daukar matakin gaggawa a lokacin da ya dace tare da raba wa al'ummar da wannan ambaliyar ruwan ya shafa na kayan tallafin ga kimanin magidanta 1078 a garuruwa 18 wadanda ibtila'in ya rutsa dasu a karamar hukumar Nguru. 

Goje ya kara da cewa mutanen da ambaliyar ruwan ta shafa sun kasu gida uku, kuma kowane bangaren ya karbi nashi kason tallafin gwargwadon yanayi da hali. 

A hannu guda kuma, Hukumar SEMA ta kai wa yan gudun hijirar jihar wadanda suka koma yankunan su tallafi a gundumomi 5; wadanda suka hada da Dadingel, Goniri, Ngurbuwa, Gotala da Mandunari, a karamar hukumar Gujba a jihar Yobe. Tallafin da hadin gwiwa ne tsakanin Hukumar SEMA da kungiyar jinkai ta 'World Food Programme' a karkashin shirin CCDRN wanda sama da magidanta 14,200 suka ci gajiyar tallafin naira 26,600 (kowane mutum daya).

Dr. Goje ya bayyana cewa, wannan tallafin kayan abinci a irin wannan lokaci wanda Kungiyar WFP ta aiwatar ya zo a lokacin da yan gudun hijirar ke bukatarsa, a sa'ilin da jama'ar yankin ke fargabar fita gonakinsu sakamakon barazanar tsaro, tare da ibtila'in ambaliyar ruwan da ya mamaye wasu gonakin da al'ummar yankin suka dogara dashi wajen noma abincin da zasu ci. 

Har wala yau kuma, Shugaban Hukumar SEMA ya yaba da irin kokarin da kungiyar bayar da agajin gaggawa tare da takwarorinta wajen tallafa wa al'ummar yankin, kana kuma ya yi kira ga wadanda suka samu tallafin cewa suyi amfani da kayan bisa ka'ida, yayin da kuma ya bukaci masu ruwa da tsaki wajen raba kayan su tabbata sun raba su ga wadanda suka cancanta.

"Haka kuma sanin kowa ne kan cewa wannan Hukuma ta SEMA a jihar Yobe ta na aiki ne bisa umurnin Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni kuma ya yi alkawarin ci gaba da tallafa wa al'ummar wannan jihar domin cike gibin da wadannan ibtila'in ya haifar, kokari wajen ganin an taimaki maras karfi inda abin ya shafa a jihar Yobe, kuma ya bayar da tabbacin daukar matakai a duk lokacin da irin wannan ibtila'in ambaliyar ruwa ya faru." In ji Dr. Goje.