WANI GIDA: Labarin Soyayya Mai Rikitarwa, Fita Ta Uku

WANI GIDA: Labarin Soyayya Mai Rikitarwa, Fita Ta Uku

WANI GIDA
*(GIDAN GADO)*


*RUBUTAWA DA TSARAWA*


*ZAINAB MUHAMMAD*
*(Indian Girl)*


*BIS-MILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*

*Page 5&6*

Koda ta shiga gidan ba wanda taiwa magana ta wuce ɗaki ta aje jaka da hijab ɗinta tai shimfiɗa ta kwanta,itama Mama bata koma ta kanta ba.

*Washe gari*


Da wuri Nufaisat tai shirin makaranta domin ranar jarrabawar 7:00Am dao dai suke da ita,Nufaisat tana sa fushi da zuciya amma fushinta baya wuce zuwa lokacin da za tai bacci.

Mama ta gaisar sannan tabi mutanan gidan ta gaisar,sannan ta tafi makaranta.

Sunyi jarrabawa sun gama ta taho hanya a gajiye likis ga yunwa ga gajiya ta kwaso dake dama ba taci abinci ba ta fito,kuma Mama bata da kuɗi.


Har ta ɗan gota wani dandamali sai kuma ta dawo,wani matashin saurayi ta gani Iya haɗuwa ya haɗu sai dai wahala duk ta mai daahi wani kala,zaune a gun ya yi tagumi da hannuwa bibbiyu hawaye yana zubo masa.


"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un"

Shine kalmar data fito daga bakin Nufaisat,ta koma da baya tare da ƙure shi da ido ba zaka taɓa gane tsananin kyawun da yake da shi ba sai ka nutsu.

Durkusawa Nufaisat tayi kusa dashi tare da ɗan bubbuga hannunsa,a zabure ya kalleta tare da kureta da ido.

Tsarki ya tabbata ga ubangijin halittar daya halicci wannan ma'abociyar kyawun,sai kuma ya ɗan ja baya a tsorace(karfa yaje aljanace domin wannan kyaun ya yi yawa kamar na ɗiyar aljanu).g

Shiru ya yi a cikin ransa yaji kawai ya yarda da yarinyar ya faɗa mata damuwarsa,dan haka sai ya faɗa mata"Ni talakane an kama mahaifiyata akan bashi wanda bai taka kara ya karya ba kuma ance nakai nan da kwana biyu idan ba haka ba za a sake kamata saina kai kuɗin"


Shiru Nufaisat tayi tana tunani*me yasa wasu mutanan basa da tausayi ko kaɗan?me yasa masu bashi ba zasu dinga ɗagawa waɗanda suke bi bashi ƙafa ba? duniya fa ba matabbata bace idan kaine yau ba kaine gobe ba"


"Na san mai min maganin matsalata sai ubangijina"

Nufaisat ta jiyo muryarsa yana faɗar haka.

Tace"Kuɗin har nawa ne?"

A jiyar zuciya ya sauƙe da,Cewa"3k ne"


Jinjina kai Nufaisat tayi kafin,Tace"Dubu uku? akan dubu uku?"

*Cabb gaskiya idan Allah yai mata arziƙi al-umma zasu huta domin ba zata taɓa bari taga wani cikin damuwa ba ko zubda hawaye,zata taimaka masu iya ƙarfinta zata sa su dariya da izinin Allah*

Duk wannan maganar Nufaisat a ranta take faɗe,amma bata sani ba kukan zucine ya fito fili,sai ji tai yana,Cewa"Allah ya baki iko bake kaɗaiba har ma da masu niya"


Murmushi Nufaisat tayi tare da sunkuyar da kai kasa tana wasa da gefan hijab ɗinta.


"Ka tashi muje kaga gidan mu ka tsaya na fito na kawo maka,Amma dan girman Allah kar kacemin a'a"

Ta faɗi haka tana kallonsa.


"Shikenan nagode Allah ya biyaki ya rayaki ya biya maki buƙatunki yasa ki gama da iyayenki lafiya ya cika maki burukanki"


Ameen kawai Nufaisat take cewa saboda taji daɗin addu'ar da yai mata.

Haka suka jera suna tafiya anan Nufaisat take bashi labarin cewa ai mahaifinta ya rasu gashi yayan mahaifinta azzalumine suna dai zaune cikin maƙiya.

Ya tausaya masu baki ɗaya har shi kansa,domin shima ba zai taɓa mantawa ba irin wannan matsalar ta sa suka shiga halin da suke ciki.

Haka sukaita hira har suka iso unguwar,cewa tayi ya tsaya taje ta dawo daga ɗan nesa da gidan nasu.


Haka kuwa aka yi tana shiga gidan ta sami Raudat ƙanwarta ta tambayeta ina Mama? Raudat tace sun tafi unguwa da Umma.

Jin haka yasa ta shige ɗaki,bankinta da take ajir kuɗi ta ɗauko ta fafe shi ta ciro kuɗaɗan ciki ta haɗe su tare da lissafawa,2600 ne ba haka taso ba taso ace dubu ukun ne amma ya zatai.

Miƙewa tayi ta fice a ind tace ya tsaya anan ta same shi,miƙa masa kuɗin tayi tare da,Cewa"Kaga Mamanmu bata nan amma na fafe bankina sai dai basu kai ba 2600 ne kayi haƙuri"


Murmushi ya yi da Cewa"Nagode sosai ƙanwata amma ki riƙe naira 100 a hannunki"

Girgiza kai Nufaisat tayi da,Cewa"Wallahi ba zan karɓa ba na baka"

Godiya sosai ya yi mata tare da alƙawarin zai dinga kawo mata ziyara.