Sace Biliyan 189: An Roki Tambuwal Ya Shigar Da Maganar Gaban Kotu In Har Sheri Aka Yi Masa

Sace Biliyan 189: An Roki Tambuwal Ya Shigar Da Maganar Gaban Kotu In Har Sheri Aka Yi Masa

Wasu masu sharhi kan al'amurran yau da kullum a jihar Sakkwato sun shawarci gwamnan Sakkwato ya dauki mataki mai tsauri kan wanda yake ganin ya yi masa sharri na zargin Gwamna da wasu mukurabansa sun yi sama da fadi na biliyan 189 a cikin kudaden da suka karba na al'ummar jihar Sakkwato.

Dakta Bashir Achida ya ce akwai alamun gaskiya a cikin rahoton ɓatar da kudin domin kamata ya yi, su ji tsakanin gwamnati da masu rahoton suna kotu ba a tsaya kan yin raddi ba, da fadin akwai hujjoji 'kotu yakamata a gayawa.'
"Abin da muke son gwamnati ta yi a gaya mana duk abin da gwamnatin nan(ta Tambuwal) ta karɓa na ƙananan hukumomi da jiha, muna ƙalubalantar gwamnati a fitar da bayani kan kudin da ta karba ta yi wa Allah tun da mai gaskiya ce buga a jarida don Nijeriya ta san Tambuwal mai gaskiya ne a zaɓe shi shugaban kasa,' a cewar Achida. 
Dakta Mansur Isah Buhari ya ce "in zargi ne ake yi gwamnati ce ta ba da dama, mu ba bukatarmu gwamnati ta yi rubutun ƙaryatawa ba, mu ga an kai gidan jaridar da suka  fitar da bayanin kotu kan ɓata sunan gwamna Tambuwal.
"A yi lissafi a shekara bakwai an karɓi kudin sun fi naira biliyan 500 a Sakkwato a fadi nawa aka kashe a al'bashi da aiki da bashi. Duk wanda ya yi wa gwamna ƙazafi yakamata a dauki  mataki a hukumance kansa," a cewar Dakta Mansur.
Barista Mu'azu Liman Yabo ya ce in dai zargin sun batar da kudi kazafi ne tau su garzaya kotu kan maganar.
Da fari an fito da wata takarda dake yawo a kafofin sada zumunta ta ce Gwamnatin jihar Sokoto ta Aminu Waziri Tambuwa ta sace tare da karkatar da kimanin Naira biliyan 189 daga asusun gwamnati da wasu mutane masu zaman kansu, kamar yadda takardar da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) da Babban Bankin Najeriya (CBN) ta bayyana.
 
Takardar mai dauke da sa hannun DCE AS Abubakar ta kuma aika wa shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa ta yi zargin cewa an bankado wasu asusun 'yan kasuwa wanda ke da alaka da asusun Gwamnatin Jihar Sakkwato daga ranar 1 ga watan Janairun 2015 zuwa 31 ga Agusta, 2021.
 
A cewar Abubakar, asusun ya samu jimillar kudaden da suka kai N567,160,024,619.93 a cikin wannan lokacin inda aka karkatar da N189,155,043,825.09 ba bisa ka’ida ba.
 
Wannan rahoton ne gwamnatin Sakkwato ta karyata tare da fadin duk wasu hujja da aka fadi a rahoton a jefar da shi.
Wannan bayani an samar da shi ne domin a bata sunan Tambuwal a takarar shugaban kasa da yake yi.