Hadimin Gwamna  ya raba wa mata masu karamin karfi Atamfofi 100 a Yobe

Hadimin Gwamna  ya raba wa mata masu karamin karfi Atamfofi 100 a Yobe

Daga Muhammad Maitela, Damaturu.

Mataimaki na musamman ga Gwamnan jihar Yobe kan harkokin ilimi a matakin farko da sakandire, Hon. Isa Ba-malum Bashir ya kaddamar da raba wa mata masu karamin karfi atamfofi kyauta a Gashu'a, shalkwatar karamar hukumar Bade a jihar Yobe. 

Da yake mika tallafin ranar Asabar, a Asibitin Kwararru (Specialist Hospital) Gashu'a, Hon. Ba-malum ya ce wannan shi ne karo na uku da yake aiwatar da raba tallafin zannuwan atamfa ga mata masu karamin karfi domin taimaka musu, duba da halin da jama'a suke ciki, musamman mata.

"Sannan kuma a matsayina na dan siyasa, nayi tunanin hakan zai taimaka ganin cewa bai kamata ace komai sai gwamnati tayi wa mutane ba. Muma ya dace mu tallata wa jama'a a matsayinmu na wakilan jama'a kuma idon Mai Gidsnmu, Gwamna Mai Mala Buni, kuma ya dace mu kasance wakilai nagari tsakanin sa da jama'a."

 "Har wala yau, kowane lokaci kiran da Gwamna Buni yake mana shi ne ya bamu dama ce domin muma mu taimaki wasu a matsayinmu na wakilan sa a tsakanin al'ummar jihar Yobe. Wannan ne ya bani kwarin gwiwa wajen tallafa wa jama'a da dan abin da nake samu." In ji Hon. Ba-malum.

Ya kara da cewa, "Yanzu a nan Asibitin Kwararru mun raba wa mata 50 zannuwan atamfofi kyauta, daga bisani kuma za mu ci gaba da raba sauran 50 kuma zamu bisu gida-gida a unguwanin su mu basu kamar yadda muka tsara." 

Hon. Bashir ya bayyana cewa ya zabi bayar da wannan tallafin ga mata ne sakamakon yadda suke bayar da gagarumar gudumawa a kowane fannin rayuwa, tare da kuma yadda ake taka rawar gwagwarmayar siyasa dasu amma a manta dasu.