Kalaman Malami Sun Bayyana Yanda Yake Wa Alƙalai Katsalandan A Shari'ar Da Yake So-----Bajare

Kalaman Malami Sun Bayyana Yanda Yake Wa Alƙalai Katsalandan A Shari'ar Da Yake So-----Bajare

Tsohon dan majalisar dokokin jihar Sakkwato Malami Muhammad Galadanci da aka fi sani da Bajare ya maganta kan rikicin shugabanci da jam'iyyarsu APC take fama da shi a Sakkwato in da ministan shari'a ya bayyana matsayar shi ga wani bangare daban saɓanin nasu da suka yi zaɓe.
Bajare a zantawarsa da Managarciya ya ce kalaman Ministan shari'a kan shugabancin APC a Sakkwato sun bayyana yanda yake wa alƙalai katsalandan a shari'ar da yake so hujja kan haka magana tana gaban kotu ba a yanke hukunci ba amma ya zo ya ce ga wanda shari'a ta baiwa halastacce wanda ba haka ba ne.
"wannan katsalandan ne ya yi wa alƙali don ya nunawa duniya cewa a matsayinsa na ministan shari'a sai yanda ya so alƙalai ke yi wanda mu mun san ba haka ba ne, alƙalai mutane  ne masu daraja da sanin yakamata da ke yi ƙasa aiki ba ruwansu da duk wani mai riƙe da muƙamin je-ka na-yi-ka.
"minista ya bayyanawa al'umma kasawarsa da kuma ɗaura ƙiyayya ga wanda ya taimaki siyasarsu waton Sanata Aliyu Wamakko a 2015 da yake rigima sai APC ta samu mulki a lokacin Minista ɗan ta yi daɗi ne, ya sani hulɗar abokantaka ba ta hawa saman gaskiya da ma'abota halacci," a cewar Bajare.
Ya ce alƙalai ya kamata su ƙara riƙe martabarsu da koya hankali ga duk wanda ya shiga gabansu a shari'ar da ke gabansu hakan zai sa martabar shari'a ta ɗore  kuma samu zaman lafiya a Nijeriya.