Har yanzu ba mu ga tirela 20 ta shinkafa da gwamnatin Tinubu ta ce ta aiko mana ba- Jihar Abia
Gwamnatin jihar Abia ta ce har yanzu gwamnatin tarayya bata bayar da tirelar shinkafa 20 ba ga jihar.
Kwamishinan yada labarai na jihar, Prince Okey Kanu, ya shaidawa jaridar Vanguard cewa babu wani tallafi irin wannan da ya isa jihar inda ya kara da cewa gwamnatin tarayya bata tuntube su kan cewa za ta aiko da tallafi.
Haka kuma ya musanta cewa gwamnatin ta tarayya ta raba shinkafa ga jihohi domin siyarwa kan Naira dubu 40.
Ya ce "Bamu ga ko mota daya ta shinkafa ba daga gwamnatin tarayya. Sannan maganar siyar da buhun shinkafa kan Naira dubu 40 labaran kanzon kurege ne".
Ya ce akwai hanyar da gwamnatin tarayya ke tuntubarsu idan akwai tallafi irin wannan, amma har yanzu babu batun aiko da tallafi jihar.
Hakan na zuwa ne dai yayin da ministan yada labarai, Mohammed Idris ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta raba motar shinkafa Tirela 20 ga kowacce jiha domin saukakawa al'umma.
Ko a kwanaki ma sai da gwamman jihar Oyo, Seyi Makinde ya musanta karbar kudi Naira Biliyan 570 daga gwamnatin tarayya zuwa jihohi.
managarciya