Daga Awwal Umar Kontagora, Abuja.
Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya gana da shugabannin hukumomin kula da harkar ilimi na tarayya don daƙile wutar da ke ruruwa a bisa zargin ƙarin kuɗaɗen makaranta da wasu manyan makarantun ƙasar nan suka yi.
Waɗanda suka halarci ganawar da aka yi a ranar Talata nan a Abuja sun haɗa da babban sakataren hukumar kula da jami'oi (NUC), Professor Abubakar Rasheed, babban sakataren hukumar kula da kwalejojin ilimi (NCCE), Professor Paulinus Chijoke Okwelle da Hajia Bilkisu Salihijo Ahmad da ta wakilci hukumar kula da ilimin fasaha (NBTE).
A jawabin sa na buɗe taron, shugaban majalisar dattawan yace ya kira taron ne a bisa ƙorafin da ɓangaren ɗalibai na haɗaɗɗiyar ƙungiyoyin Arewa suka gabatar masa na shirin wasu manyan makarantu na ƙara kuɗin makaranta.
Bayanin bayan zaman taron na ƙunshe a wata takardar manema labaru, da ma baiwa shugaban majalisar dattawa shawara akan aikin jarida, Ola Awoniyi ya sanyawa hannu.
Ya cigaba da cewar "Ya zama mana dole mu saurari ɗaliban mu, mu kuma saurare ku don gano gaskiyar al'amarin.
"Duk halin da muka samu kan mu a ciki, dole ne mu yi duk abinda za mu iya yi wajen ganin ba mu yi abinda zai jefa ɗaliban mu cikin halin wahala ba.
"Mun sani cewa manyan makarantun mu suna baƙatar ƙarin kuɗaɗe, amma duk da haka mun san cewa da yawan ɗaliban mu ƴaƴan takakawa ne kuma dole ne mu yi duk mai yiwuwa don kare su.
"Bai kamata a ce matsalar kuɗi ta zama sanadin hana yaran mu cim ma burin su ba. Dan haka, dole ne mu gano yadda matsalar ta ke da matakan da za'a ɗauka wajen shawo kanta".
Shugaban ya ba ɗalibai tabbacin cewa a kowane lokaci majalisar dokoki ta ƙasa da ma gwamnati za su yi aiki tuƙuru wajen ba su kariya da goyon baya.
Da yake mayar da jawabi a madadin sauran, babban sakataren NUC, Professor Rasheed ya yaba ma shugaban majalisar bisa shigar sa cikin maganar.
Yace suma hukumonin sun damu akan al'amarin, yana mai cewa, " A halin yanzu yana da wahala a gane wace makaranta ce ta saɓa ƙai'ida".
Ya bada tabbacin hukumomin zasu gaggauta yin bincike don sanin ainihin abinda ke faruwa.