Dan Aikin Gida Ya ɗirkawa ɗiyar Mai Gida Ciki, Ya ƙona ta ƙurmus Bayan An  Samu Akasin  Zubar Da Ciki

Dan Aikin Gida Ya ɗirkawa ɗiyar Mai Gida Ciki, Ya ƙona ta ƙurmus Bayan An  Samu Akasin  Zubar Da Ciki

 

YOLA 24

 

Wanda ake zargin, Munkaila Ado, ya ɗirka wa yarinyar ciki sannan ya haɗa baki da mahaifiyar ta domin kai ta jihar Gombe a zubar da cikin. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.

 
Kakakin hukumar, SP Ahmed Wakil, a ranar Asabar 13 ga watan Agusta, 2022, yace an cafke wasu mutum biyu ciki har da matar da ta bayar da abin zubar da cikin. 
 
A cewar Wakil, bayan samun nasarar zubar da cikin mai wata huɗu, wanda ake zargin da abokin sa sun maƙare yarinyar, sannan suka ƙona jikinta ƙurmus tare da birne ta a cikin wani ƙaramin rami a cikin daji.
 
Mahaifin yarinyar ya shigar da ƙorafin ɓacewar ta
 
Kakakin ƴan sandan yace, mahaifin yarinyar wanda ya lura da cewa yarinyar sa ta ɓace kuma yana zargin ɗan aikin gidan da abokin sa, sai ya miƙa rahoton lamarin a ofishin ƴan sanda na Alkaleri.
 
A ranar 10/08/2022 da misalin ƙarfe 9 na safe, wani Alhaji Danladi Mohammed, daga ƙauyen Mai’ari Arewa Pali, ya shigar da ƙorafi a ofishin ƴan sanda na Alkaleri, cewa a ranar 04/08/2022 ɗiyar sa mai suna Safiya Alhaji Danladi ƴar shekara 13, ta bar gida inda akayi zargin ta ɓace sannan yana zargin cewa ɗan aikin gidan sa mai suna Munkaila Ado mai shekara 27 da wani Muazu Umaru mai shekara 35, sune waɗanda yake zargin sanin inda ƴar sa ta ɓace. A cewar sanarwar
 
Nan da nan aka fara gudanar da bincike, DPO na Alkaleri yaje wurin da aka birne yarinyar sannan aka tono ta inda aka kai ta babban asibitin Alkaleri, inda likita ya tabbatar da ta rasu
 
A yayin da ake masa tambayoyi, wanda ake zargin ya bayyana cewa yarinyar budurwar sa ce kuma tana ɗauke da cikin wata huɗu da sanin mahaifiyar ta amma mahaifin ta Alhaji Danladi Mohammed bai sanda cikin ba.
 
Ɗan aikin gidan ya haɗa baki da mahaifiyar yarinyar suka bata maganin zubar da cikin Wanda ya kaiga rasa rai.