Yara Miliyan 20 Da Basa Zuwa Makaranta Ka Iya Zama 'Yan Boko Haram A Najeriya----Obasanjo

Yara Miliyan 20 Da Basa Zuwa Makaranta Ka Iya Zama 'Yan Boko Haram A Najeriya----Obasanjo

Daga Abbakar Aleeyu Anache.

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya yi gargadin cewa wajibi ne gwamnatin kasar ta dauki matakan gaggawa wajen magance matsalar tarin kananan yaran da ake da su wadanda basa zuwa makaranta ko kuma a fuskanci karuwar mayakan Boko Haram miliyan 20,

A jawabinsa gaban taron kasa kan sauya fasalin tsarin ilimi mai zurfi da majalisar wakilan kasar ta shirya Obasanjo ya ce matukar ba a dauki matakan da suka dace wajen mayar da yara miliyan 20 makaranta ba ko shakka babu akwai hadarin su iya tsunduma cikin kungiyoyin yan ta'adda, 

Taron wanda ya gudana a Abuja ya mayar da hankali kan kalubalen da yajin aikin kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ASUU ke haifarwa ga rayuwa ko kuma makomar daliban kasar, 

Tsohon shugaban na Najeriya Olusegun Obasanjo ya ce wajibi ne gwamnati ta bullo da wasu shirye-shirye da za su rage yawan yaran da basa zuwa makaranta don dakile barazanar yiwuwar fadawarsu mugayen hannu, 

Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa yaran da basa zuwa makaranta babu ta hanyar da za su iya taimakawa wajen gina ksa dalilin da ke nuna bukatar da ake da ita wajen tilastawa yara karatu don cigaban kasar,

A cewar Obasanjo akwai bukatar tilasta zuwa makarantun Firemare da Sakandire ga dukkanin yaran Najeriya yana mai cewa gwamnati ta gaza wajen iya rage yawan yaran da basa zuwa makaranta musamman a arewacin kasar da ake fama da matsalolin ta'addanci,

Cikin yara miliyan 244 da basa zuwa makaranta a sassan duniya Najeriya ke da adadin yara miliyan 20 da ke matsayin kashi 10, na jumullar yaran marasa zuwa makaranta,