Dalilin da ya sa ba zan halarci taron tattaunawa da ƴan takarar shugabancin ƙasa ba--Kwankwaso

Dalilin da ya sa ba zan halarci taron tattaunawa da ƴan takarar shugabancin ƙasa ba--Kwankwaso

 

Dan takarar shugaban kasar Najeriya karkashin jam'iyyar NNPP, Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso, ya ce ba zai halarci taron tattaunawa da 'yan takarar shugaban kasa da hadakar kungiyoyin Arewacin kasar suka shirya, saboda zarginsu da goyon bayan wani ɗan takarar na daban.

 

Wasu hadakar kungiyoyin arewacin kasar da suka hadar da kungiyar Arewa Consultative Forum, da kungiyar Arewa House, da gidauniyar Sir Ahmadu Bello, da kungiyar Northern Elders Forum da kuma kungiyar Arewa Research and Development Project ne suka shirya taron tattaunawar tsakanin 'yan takarar shugabancin kasar.
 
A wata sanarwa da mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben dan takarar Abdulmumin Jibrin, ya sanya wa hannu, ya kuma wallafa a shafinsa na Tuwita ya ce, ya bayyana cewa Kwankwaso ya riga ya shirya yakin neman zabe a ranar da aka tsara zai yi jawabi a taron.
 
Sannan kuma sanarwar ta yi zargin cewa sun sami sahihin labarin da ke cewa wasu daga cikin masu shirya tattaunawar na da wata manufa, sannan kuma za su yi amfani da taron ne wajen nuna goyon baya ga wani dan takara
 
An dai tsara cewa Kwankwaso zai yi jawabi a gaban taron tattaunawar ranar Litinin, tare da dan takarar jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu da kuma Peter Obi na jam'iyyar Labour, a yayin da tuni Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya riga ya gabatar da nasa jawabin.