‘Yan Kasuwa Sun Fara Saida Fetur a Sabon Farashi Inda Lita Ta Koma N770 a Depo

‘Yan Kasuwa Sun Fara Saida Fetur a Sabon Farashi Inda Lita Ta Koma N770 a Depo

 

Kungiyar dillalan man fetur ta kasa (IPMAN) ta bayyana cewa masu tashoshin mai (masu zaman kansu) sun kara kudin fetur zuwa Naira 770 kan kowace lita.

Shugaban IPMAN na kasa, Abubakar Maigandi ne ya bayyana hakan, inda ya bayyana cewa masu depo-depo na korafin cewa farashin dakon fetur ya karu. 
Maigandi ya ce karuwar kudin dakon fetur ya yi tasiri ga farashin man fetur a fadin kasar duk da yanzu yana samuwa sosai, jaridar The Nation ta ruwaito. 
Shugaban na kungiyar IPMAN ya ce karin kudin dakon ya haifar da sauye-sauyen farashin man fetur, wanda ya shafi farashin da gidajen mai ke bayarwa. 
A cewarsa, farashin dakon fetur a Legas ya kai kusan N30 ko N35 kan kowacce lita, yana mai jaddada cewa kudin man fetur a Legas ya kai N800 kan kowace lita yanzu. 
Maigandi ya ce masu dakon man fetur daga jihar Kebbi na biyan kudin da ya kai N70 a kowace lita, wanda hakan ya sa ake sayar da mai a kan N900 da kuma N1,000 kan kowace lita a Kebbi da Sokoto. 
“Yanzu akwai man saboda an rage yawan masu siya. Amma matsalar ita ce masu depo sun kara kudi. Yanzu suna ba da lita 1 a kan N770. 
“A wannan yanayin, farashin fetur din zai danganta da garin da mutum yake. A jiha mafi kusa kamar Lagos, za ka biya kudin dako N30, ka ga lita za ta koma N800 kenan.