Manoma Da Makiyaya 'Yan Uwan Juna Ne Ya Kamata Su Zauna Lafiya-----Inji Babayo

Manoma Da Makiyaya 'Yan Uwan Juna Ne Ya Kamata Su Zauna Lafiya-----Inji Babayo

Daga Awwal Umar Kontagora, a Minna.

An kira ga makiyaya da manoma da su zauna lafiya a tsakaninsu domin dukkan su yan uwan juna ne. Fitina da rashin hakurin zaman tare ba zai haddasa komai ba face koma baya a tsakanin su, mun sani zumuncin da ke tsakanin su tamkar hagu da dama ne a mu'amala. Darakta Janar mai kula da harkar ilimin makiyaya da zaman lafiya a jihar Neja, Ardo Abdullahi Adamu Babayo ne ya bayyana hakan ga manema labarai a minna.

Ya kamata mu koma kan tsohuwar al'adar mu na zumunci da kaunar juna tsakanin manoma da makiyaya, kamar yadda muka faro, domin shi ne hanyar da za a iya dawo da zaman lafiya.
Manoma su kiyayi taushe buggalai da burtalai domin makiyaya su samu hanyar wucewa da dabbobin su, su ma makiyaya su guji tura dabbobin su suna cin anfani gona, domin halin da muke ciki yau sakin wannan hanyar ce ya janyo mana shi.
Bai yiwuwa, wani batagari marar abin yi na zaune cikin gari bai da aikin da ya wuce amsar beli a hannun yan sanda ya barku ku zauna lafiya, domin wannan mugun hanyar da ita ya dogara, kuna kashe miliyoyin kudi wajen kara ga yan sanda da alkalai, yayin da ku kara talaucewa da rashin kwanciyar hankali a matsugunnan ku.
Dan haka ina kira da babban murya ga yan uwana makiyaya da manoma, duk abinda ya taso mu rika zama muna yin sulhu a tsakanin mu, ba sai mun tafi ofishin yan sanda ko alkalai ba, in har da gaske muna son zaman lafiya da zaman tare a tsakanin mu.