Uwargidan Ganduje Gwaggo ta nuna wanda zai gaji mijinta
Hafsat Ganduje, uwargidan Gwamna Abdullahi Ganduje ta nuna wasu alamu da ke nuna wanda zai gaji mijinta a wurin taro a ƙaramar hukumar Ungogo ta ce Murtala Sule Garo mutum ne da ya san yakamata.
A lokacin da take magana ga jami'an gwamnati da waɗanda suka amfana da shirin koyar da sana'a Gwaggo ta ce Garo ya haɗa dukkan abubuwan da Ganduje ke so ga wanda zai gaje shi
Ta ƙara dacewa a lokacin da tayi tafiya tare da Garo a lokacin ta gamsu ya kamata ya gadi mijinta a shekarar 2023.
Ta ce ko shugabannin ƙananan jukumomi da aka zaɓa sai da aka zaƙulo domin gwamna bai son ciyaman da baya da kwarewa.
managarciya