Jigo a Jam'iyar APC Ya Sauya Sheka Zuwa PDP a Sakkwato

Jigo a Jam'iyar APC Ya Sauya Sheka Zuwa PDP a Sakkwato

Daya daga cikin jigo ajam'iyar APC Honarabul Ibrahim Dasuki Haske ya sauya sheka zuwa jam'iyar PDP mai mulki a jihar Sakkwato.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ne ya karbi tsohon shugaban karamar hukuma Sakkwato ta kudu kuma tsohon dan majalisar dokokin jiha Ibrahim Haske a fadar gwamnatin jiha.

Sauya shekar ta zo da bazata ganin yanda jigon ya tabbatar da zamansa a tsohuwar jam'iyarsa, kasa da wata daya kuma ya watsar da tafiyar ta adawa ya rungumi gwamnati.
Haske yana da tasiri a siyasar karamar hukumar Sakkwato ta kudu abin da ake ganin gibi ne jam'iyar APC ta samu a yankin.

Bayyanar hotunan da aka dauka a fadar gwamnati ya nuna sauya shekar karara kafin gudanar da bukin karbarsa tare da magoya bayansa abin da ake ganin za a yi nan ba da jimawa ba.