Sakon Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteres na Shiga Sabuwar Skekara

Sakon Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteres na Shiga Sabuwar Skekara


Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira mai karfi yayin da ake shiga sabuwar shekara, yana gargadin cewa duniya tana tsaye a mashigin hanya.

“Yayin da muke shiga sabuwar shekara, duniya tana tsaye a kan mashigin hanya. Rikice-rikice da rashin tabbas sun kewaye mu. Rarrabuwar kawuna. Tashe-tashen hankula. Lalacewar yanayi. Da kuma take hakkin dokokin kasa da kasa. An fara ja da baya daga ka’idojin da ke hada mu a matsayin ɗan Adam.

“Mutane a ko’ina suna tambaya: Shin shugabanni suna sauraro kuwa? Shin sun shirya daukar mataki?

“Kudin da ake kashewa a harkokin soji ya haura dala tiriliyan 2.7, ya karu da kusan kashi 10%. Wannan ya ninka sau goma sha uku fiye da dukkan tallafin ci gaba, kuma ya yi daidai da dukkanin kudin shiga na nahiyar Afirka. 

“Duk wannan yana faruwa ne a lokacin da rikici ya kai matakin da ba a taba gani ba tun bayan Yaƙin Duniya na Biyu” in ji shi. 

Mista Antonio ya kara da cewa; “A wannan sabuwar shekara, mu daidaita fifikonmu. Duniya mai aminci tana farawa da zuba jari wajen yaki da talauci fiye da yaki da yaƙe-yaƙe. Dole ne zaman lafiya ya yi nasara”.

A bayyane yake cewa duniya tana da albarkatu da za su daga rayuwa, su warkar da duniya, su kuma tabbatar da makomar zaman lafiya da adalci.

“A shekarar 2026, ina kira ga shugabanni a ko’ina: Ku dauki al’amura da muhimmanci. Ku zabi mutane da duniya fiye da ciwo. Ina kuma rokon kowa da ya ji wannan sako: Ku taka rawar ku. Makomar mu tana dogara da jarumtarmu na hadin gwiwa wajen daukar mataki.”

“A wannan sabuwar shekara, mu tashi tare: Domin adalci. Domin ɗan Adam. Domin zaman lafiya.”