Buhari Ya Umarci Malami Da Amaechi Da Sauransu Da Su Ajiye Muƙamansu

Buhari Ya Umarci Malami Da Amaechi Da Sauransu Da Su Ajiye Muƙamansu

Buhari Ya Umarci Malami Da Amaechi Da Sauran Ministocin da Ke Son Tsayawa Takara Da Su Ajiye Muƙamansu

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya umarci ministocinsa dake son tsayawa takara a muƙamai daban daban a shekarar 2023 da su ajiye muƙamansu daga yanzu kafin ranar Litinin.

Shugaban ya ba da unsrnin a zaman majalisar zartarwa ta ƙasa da ya gudana yau Laraba.

Ministan yaɗa labarai Lai Muhammad ya sanar da hakan bayan zaman majalisar zartarwar.
Ministocin da ke son yin takara sun haɗa da ministan shari'a Abubakar Malami da sufuri Amaechi da ƙwadago da ƙarami na ilmi da sairansu.