'Yan Ta'adda za Su Shiga Uku, Ministan Tsaro da Hafsoshin Sojoji Sun Isa Sakkwato 

'Yan Ta'adda za Su Shiga Uku, Ministan Tsaro da Hafsoshin Sojoji Sun Isa Sakkwato 

'Yan Ta'adda za Su Shiga Uku, Ministan Tsaro da Hafsoshin Sojoji Sun Isa Sakkwato 


Karamin Ministan tsaro, Dr. Bello Matawalle ya shiga gaba inda ya jagoranci hafsoshin tsaron kasar nan zuwa babban jihar Sakkwato kan rashin tsaro. 
A baya, gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta umarci hafsoshin tsaron su tare a jihar Sakkwato domin fatattakar miyagun da su ka hana mazauna garin sakewa. 

A sakon da Bashir Ahmad, hadimin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya wallafa a shafinsa na X, ya nuna cewa shugabannin tsaron sun sauka a jihar Sakkwato a yau Talata.
Ya bayyana cewa zuwa jihar Sakkwaton ya biyo bayan shirin da ake yi na dakile 'yan ta'adda da ke jihar domin magance matsalar tsaro. 
Channels Television ta wallafa cewa hafsan hafsoshin kasar, Janar Christopher Musa da sauran jagororin tsaro sun sauka a jihar Sakkwato. An hango Janar Christopher Musa da wasu shugabannin tsaro tare da karamin Ministan tsaro kuma tsohon gwamnan Zamfara, Bello Matawalle a Sakkwato. 
Matakin wani shiri ne na tsaurara tsaro da tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a jihohin Arewa ciki har da Zamfara, Kebbi, Sakkwato, Katsina da sauran jihohi a yankin.