A jihohin arewa maso yamma yankin Sakkwato kenan za a rika sayar da kowace litar fetur kan kudi Naira 184, an samu karin kudi naira 19 a kowace litar kenan.
Naira 189 a yankin arewa maso gabas an gefen sun samu karin naira 24 ga kowace litar.
A arewa ta tsakiya za a sayar da kowace lita kan naira 179 an samu karin naira 14.
A kudu ta yamma za a rika sayar da lita kan 179, an samu karin naira 14.
A kudu maso kudu kuma litar kan 179 an samu karin naira 14.
A yankin kudu maso Gabas za a rika sayar da litar man fetur din kan farashi naira 184 karin naira 19.
A Abuja litar za a rika karbar kudinta kan naira 174, sun samu karin naira 9.
A jihar Lagos in da a can ne ake dakon man fetur din farashinsa ya koma kan naira 169 an kara naira 4 kenan a farashin baya da ake sayarwa 165.
Jaridar Daily Trust wacce ta ce ta samu tabbacin karin a Talatar nan.
Shugaba Buhari ya ce sun mika kamfanin man ne a hannun 'yan kasuwa gaba daya.