Gwamnati za ta horar da matasa 8,000 a ƙananan hukumomi 774

Gwamnati za ta horar da matasa 8,000 a ƙananan hukumomi 774

Gwamnatin Najeriya za ta horar da Sama da Matasa 8,000 da Mata a Kananan Hukumomi 774 kan Samar da Sana'o'i dogaro da kai.

Hukumar samar da aikin yi ta kasa (NDE), ta shirya horar da matasa da mata sama da 8,000 a fadin kananan hukumomin kasar nan 774.

Darakta Janar na NDE, Silas Agara ne ya bayyana haka a garin Lafia babban birnin jihar Nasarawa lokacin da ya jagoranci tawagar gudanarwa na hukumar a ziyarar ban girma ga gwamna Abdullahi Sule a gidan gwamnati.

Darakta Janar na NDE ya bayyana cewa, Darakta a karkashin gwamnatin Tinubu ta shirya tsaf don horar da matasa da mata 10 daga kowace Unguwa a fadin kananan hukumomin kasar nan guda 774 a cikin sana’o’i 30 daban-daban, domin su samu sana’o’in dogaro da kai.

Daga Abbaka Aleeyu Anache