Fassara: Hon. Buhari Sallau Hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari Bangaren Rediyo da Talabijin.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari Ranar Talata a Abuja ya bukaci dukkanin Shugabannin Jam'iyun Siyasa dake a Ƙasar dasu aje abinda ya shafi zabe da duk wata banbanci a gefe kana su hada gwiwa da Gwamnatin don jagorantar cimma nasarar yakar Matsalar tsaro a Ƙasa.
Da yake magana a yayin liyafar buda baki tare da Membobin Ƴan kasuwa da Shugabannin Jam'iyun Siyasa, Shugaban kasa ya bayyana Matsalar tsaro dake addabar Ƙasa, a matsayin 'matsala data shafi kowa'
"Ba tare da samun goyon bayan Al'umma ga kokarin da Jami'an tsaron mu ke yi ba, zai dauke karin lokaci mai yawa kafin kammala samun nasara da muke samu akan yaki da Ta'addanci, Ɓarayin daji da masu Garkuwa da Mutanen.
Dole Mu samar da zama lafiya a Ƙasar mu don Cigaban tattalin arziki ya samu gindin zama.
"Ina sa idon ganin an samu Dangantaka tsakanin Jam'iyun Siyasa da Gwamnati, Musamman a wannan lokaci na kakar siyasa da gaba nan kadan za a fara yakin neman zabe"
Shugaban yayi jawabi cewa a makon da ya gabata Babban Kwamitin Gudanar wa na Jam'iyar APC ta samu cimma Manyan Nasarori a taron ta, inda ta kare da bayyana sakon cewa Jamhuriyar zata ci gaba da matsawa don kafa manufofin Mulkin farar hula a dukkan Matakai.
"A yau, zamu iya alfaharin cewa, muna kan tsarin da dukkanin Jam'iyun Siyasa ke samun dama neman abinda suke bukata, inda yake tafiya daidai da banbanci dake tsakanin mu na yau da kullum, da tsayawa takara a kowani mataki na Gwamnati ba tare da tsoro ko wani matsi da nuna banbancin ba".
Domin saukaka tafiyar da harkokin kasuwanci a Ƙasar, a yayin liyafar Shugaban Buhari ya faɗiwa manyan Ƴan kasuwa da Shugabannin Siyasar Ƙasar cewar, Gwamnatin sa ta taka rawar gani matuka gaya, Gurin inganta yanayin tafiya da harkokin kasuwanci a Ƙasar, ya bukaci Ƴan kasuwa masu zaman kansu dasu mara baya wa kokarin da Gwamnati keyi Gurin rage Talauci da samar da guraben aiki ga Matasa.
"Babu wata Gwamnati da ta kusanci kokarin da muka yi don samar da yanayi mai kyau daya dace da harkokin kasuwanci, ƙarami da Babban donya Bunƙasa.
‘‘Saukaka tafiyar da harkokin kasuwanci wanda duk Duniya ta shaida, ta gamsu cewa ba'a taba samun lokacin da aka saukaka damar yin kasuwanci a Ƙasar kamar a halin yanzu ba. Kuma zamu ci gaba da kara ingantawa.
Haka nan kuma zamu ci gaba da mara baya ga Bangarori kasuwanci masu zaman kansu don kara inganta da habaka tattalin arziki da samar da Sabbin guraben aiki ga Ɗunbin Al'umman mu.
"Samar da aikin yi ya Naɗa Muhimmancin Gurin daidaita da kara samar da arziki wa Ƙasar mu, aiki tare tsakanin Gwamnati da Bangaren masu zaman kansu, yana samar da damar don kara gyara rayuwar Al'umma ta Hanyoyin dake da wuyar tunanin su a lokacin daya gabata,"
Shugaban Jam'iyar APC na ƙasa Sanata Abdullahi Adamu, ya bukaci Shugabannin Jam'iyun Siyasa kan su kara duƙufar da kai, Gurin tabbatar da an samu Nasarar gudanar da zabukan 2023 cikin lumana, ya ƙalubalen cewa da suyi aiki tare don cimma manufar haka.
Abdullahi Adamu yace a Matsayin sa na Shugaba, Shugabanci na bukatar Daukan Alhaki Gurin tabbatar da samun zama lafiya da daidaituwa da kwadaita wa magoya bayan Jam'iyu da Ƴan-Nijeriya bin dokokin kasa kan abubuwan da suka jibinci gangamin neman kuri'a da zabukan.
Da yake magana a matsayin Shugabannin Sauran Jam'iyu, Engr. Yusuf Yabagi, wanda shine Shugaban Jam'iyar ADP kuma Kodineto a Hadakar Jam'iyu, Inter-Party Advisory Council (IPAC). Wanda ya bayyana Shugaban kasa A matsayin cikakken Dan siyasa, yace gayyata da shugaban kasa yayi na liyafar buda baki ya nuna cewa, Chanchnata, Girmamawa nuna sha'awar tsari mai kyau".
"A kashin Gaskiya Shugabanni Siyasa daga Jam'iyu daban daban suna zaune da kai a halin yanzu, hakan ya kara nunar da cewa kai Cikakken Dan Siyasa ne wanda yayi imani kan cigaban mulkin farar hula a Ƙasar,"
Ya sanar da cewa, Inter-Party Advisory Council (IPAC) tana shirya karrama Shugaban da lambar yabo ba" Gwarzon Dimokradiya", yadda na nuna yadda shugaban ya sanya hannu kan dokar gyaran fuska wa dokokin zabe, inda ya bayyana haka a matsayin wani mataki wanda zai tabbatar da samun gudanar da ƙarɓabben zabe cikin lumana wanda zai kunshi dukkan Jam'iyu a Ƙasar.
Akan Baban zaben gama gari dake gabatowa, Yabagi yace:
"Ya mai girma Shugaban Ƙasa, hakkin tarihi ya rataya wuyar ka, shekara ta 2023 zai zamo shekarar kammala wa'adin ka. Addu'a da muke fatan faruwar sa shine ka Jagoranci dukkan wasu al'amura da suka jibinci zabukan".
Kodineton na IPAC, wanda ya yabawa Hukumar Zabe kan sauye da gyare gyaren da tayi don tabbatar da anyi ingantaccen zabuka, ya mika roko ga Shugaban Kasa daya sanya ido kan bangaren Hukumomin tsaro a zabukan bai daya dake tafe.
"Membobin IPAC suna cikin damuwa kan aiyukan Hukumar Zabe ta INEC na cewar Dan takarar da Jam'iya ta saida zai shafe tsawon fiye da watanni Goma yana yakin neman Kuri'a a Ƙasar baki daya. Haka ba kara min aiki bane.
‘‘Muna kuma son Shugaban kasa ya duba yiwuwar Naɗa wani a matsayin Hadimi a Mai kula da Dangantakar Jam'iyu," yace, hakan zai tabbatar da ofishin na kulla alaka tsakanin ofishin shugaban Ƙasa dana Jam'iyu.
Da yake shawartan gameda irin Shugaban da Najeriya ke bukata bayan Buhari, wakilin Ƴan kasuwa wanda shine Babban Manajan Darakta na Kungiyar Sahara, Kolq Adesina, yace dole ne Shugaban Najeriya da zai zo da kudurin fatan mai kyau ga Sabuwar Najeriya bawa, kashin kanshi ba."
" Muna shirin miƙa mulki ga sabuwar Gwamnati, kuma ina bukatar cikin Girmamawa na miƙa roko ga Shugaban Ƙasa kan cewar duk wanda yazo ya nuna sha'awar Shugabanci, dole ka tambaye su gameda irin manufofin da suke dashi. Ba kawai abinda suke son yi ba, a a ta yaya suke son su yi shi.
"A kullum ƙalubalen shine ta yaya za'ayi ba son yi din ba,"
Mista Adesina, wanda yayi Godiya wa Shugaban kasa wanda ya Dabbaka zub jari kan manyan aiyukan Cigaban ƙasa a duk Fadin Kasa, ciki harda gina babbar Gadan Naija (Second Niger Bridge), Babban hanyar Mota data hada Gabashi zuwa Yammacin Kasar, da dai sauran su, ya kara karfafa bukatar dake akwai na samun Cigaban irin wannan aiyuka a Gwamnati mai zuwa.