Sifeto-Janar ya bada umarnin tura rundunar 'yan sanda na musamman cikin  birnin Abuja

Sifeto-Janar ya bada umarnin tura rundunar 'yan sanda na musamman cikin  birnin Abuja

Sufeto-Janar na ‘yan sanda, IGP, Usman Alkali-Baba, ya umurci rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, sashin dabarun yaƙi rundunar ‘yan sanda da kuma ’yan sandan da ke zaune a Abuja yankin da su sake tashi tsaye wajen tsaurara dabarun tsaro a yankunansu.

A jiya Lahadi ne ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya fitar da gargaɗi na tsaro, wanda ke nuni da cewa ana fuskantar barazanar hare-haren ta'addanci a kasar, musamman a babban birnin tarayya Abuja.

Da ya ke magantu wa a kan batun, IGP, a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya fitar, ya bayar da tabbacin tsaron lafiyar ƴan ƙasa da sauran mazauna kasar da maziyartan kasar, yana mai cewa babu wani abin fargaba, “saboda kowa yana bada gudunmawar sa wajen maganin rashin tsaro."

A cewar mai magana da yawun hukumar,  ƴan sanda, a matsayinsu na hukumar da ke jagorantar harkokin tsaron cikin gida, ba za su dauki duk wani bayanan sirri da wasa ba.

 PRO ya sanar da fara wani atisaye  na yaki da ta'addanci na gaggawa mai taken "Operation Darkin Gaggawa"

“Don haka NPF ta bukaci jama’a da kada su firgita saboda karar fashewar abubuwa da harbe-harbe a lokacin atisayen.