Kungiyar NRC Da Hadin Guiwar IFRC Sun Horar Da Mutane 50 A Gombe
Sakataren Yanki na kungiyar a jihar Gombe (Branch Secretary) Murtala Aliyu, shi ne ya shaidawa wakilin mu hakan a lokacin bada wannan horo na kwanaki uku a babban dakin taro na Asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya. Murtala Aliyu, yace sun zabi su horar da mambobin su ne guda 50 Yan sa kai hanyar koyawa jama'a yadda ake hada gishiri da suga dan bai wa wanda ya kamu da cutar Amai da gudawa agajin gaggawa da idan suka samu horon za su shiga yankunan karkara suyi aiki na watanni uku.

Kungiyar NRC Da Hadin Guiwar IFRC Sun Horar Da Mutane 50 A Gombe
Daga Habu Rabeel Gombe
Kungiyar bada agaji ta Nigerian Red Cross NRC da hadin guiwar international Federation of Red Cross and Red Cressent IFRC ta horar da Yan sa kai mutum 50 da za su shiga lungu da sako wajen wayar da mutane hanyar Kare kai daga kamuwa da cutar Amai da gudawa a Gombe.
Sakataren Yanki na kungiyar a jihar Gombe (Branch Secretary) Murtala Aliyu, shi ne ya shaidawa wakilin mu hakan a lokacin bada wannan horo na kwanaki uku a babban dakin taro na Asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya.
Murtala Aliyu, yace sun zabi su horar da mambobin su ne guda 50 Yan sa kai hanyar koyawa jama'a yadda ake hada gishiri da suga dan bai wa wanda ya kamu da cutar Amai da gudawa agajin gaggawa da idan suka samu horon za su shiga yankunan karkara suyi aiki na watanni uku.
Yace sun zabi hada gishiri da sugar ne saboda su taimakawa gwamnati wajen shawo kan cutar ta hanyar wayar da kan al'umma.
A cewar sa wannan horo sun samu tallafin kungiyar NRC ne da IFRC na duniya, amma duk da haka suna neman tallafin gwamnati dan fadada Shirin
Sakataren na Red Cross, yayi Kira ga al'umma da su koyi tsabtar jiki da ta Muhalli da Shan ruwa Mai tsabta dan gudun kamuwa daga cutar kwalera.
Sannan yace kasancewar a cikin su akwai Ma'aikatan lafiya shi yasa suka dauko su dan taimakawa wajen tabbatuwar shirin
Daga nan sai ya sake yin Kira ga jama'a da su bai wa bangaren lafiya kulawa ta musamman dan inganta rayuwar su.
Wasu da mga cikin mahalarta taron da muka zanta da su sun bayyana gamsuwar su da wannan horo inda suka ce sun karu da ilimi a wannan horo da aka basu.
Mahalarta taron an zabo su ne daga kananan hukumomin Balanga da Gombe.
managarciya