Sabon Kwamishinan 'Yan sanda ya kama aiki a Sakkwato
Rundunar 'yan sandan jihar Sakkwato ta samu sabon kwamishinan 'yan sanda CP Ahmed Musa zai karbi ragamar jagoranci hannun CP Ali Hayatu Kaigama da ya yi ritaya a aikin dan sanda.
CP Ahmed Musa dan karamar hukumar Mubi ta Arewa a jihar Adamawa ya zo Sakkwato domin aikin kare mutanen jiha da dukiyoyi da kasa baki daya.
A bayanin da jami'in hulda da jama'a na rundunar ASP Ahmad Rufa'i ya fitar ya nuna sabon kwamishinan ya soma aiki.
managarciya