HUKUMAR  MAJALISAR KADUNA TA YABAWA MAJALISAR JIGAWA BISA KYAKKYAWAN TSARIN GUDANARWA

HUKUMAR  MAJALISAR  KADUNA TA YABAWA MAJALISAR JIGAWA BISA KYAKKYAWAN TSARIN GUDANARWA

RABIU ALI.

Hukumar gudnarwar majalisar Jihar Kaduna ta yabawa da irin salon gudanarwar da majalisar Jihar Jigawa keyi kan ayyukan ta na majalisa.

Dr. Isiah Sarki Habu shugaban hukumar gudanarwar majalisar Jihar Kaduna ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ziyar ci shugaban hukumar gudanarwar majalisar Jigawa a offishin sa dake Dutse, a ranar Alhamis 23 ga watan yuni , 2022, Wanda kungiyar PERL-ECP da 'yanjaridu suka shaida.

Isiah ya ce sun je Jihar Jigawa ne domin koyon wash hanyoyin gudanarwar da majalisar Jigawa keyi kuma sun gamsu da hakan.

Ya ce sun koyi abubuwa da dama Wanda za su yi kokarin dabbakawa a Jihar su ta Kaduna domin ayyukan su na majalisa suyi kyau.

Dr. Isiah ya ce majalisar Jihar Jigawa ta samu hadin kan gwamnan Jihar Alhaji Muhammad Badaru Abubakar wajen tabbatar da cewa majalisar ta samu damar gudanar sa ayyukanta ba tare da shamaki ba.

Daga karshe ya yabawa gwaman Jigawar wajen namijin kokarin da yakeyi a Jihar Don tabbatar da alummar Jihar sun samu roman demokradiyya.

A nasa bangaren shugaban hukumar gudanarwar majalisar Jihar Jigawa Alhaji Aminu Ibrahim Babura ya ce yayi matukar jindadi da wannan ziyarar inda hakan ya ke nuna cewa jihar Jigawa ta na gudanar da ayyukan ta yadda ya Kamata.

Babura ya ce wannan yabon duka na gwamna Badaru Abubakar ne domin da sahalewar sa majalisar Jihar ta samu yancin gudanar da ayyukanta ba tare da shamaki ba.

ya ce an kafa hukumar gudanarwar majalisar ne domin ta samu 'yancin kanta tun shekarar 2018 da nufin inganta ayyukan karkara.

Shugaban ya kuma yi Kira ga alumar Jihar Jigawa musamman wadanda basi da katin zabe da su yi kokari su mallaki nasu domin zabar shugaban da ya dace a babban zabe Mai zuwa na 2023.