Bamu ƙara alawus ɗin masu yiwa ƙasa hidima ba -NYSC
Shirin kula da masu yiwa ƙasa hidima na NYSC ya mayar da martani kan wani rahoto dake yawo a kafafen sada zumunta kan cewa za a ƙara alawus din masu yiwa ƙasa hidima zuwa Naira dubu 70.
A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Eddy Megwa, Daraktan yaɗa labarai na shirin NYSC ya bayyana rahotan a matsayin na kanzon kurege.
Shirin na NYSC ya ce bai karɓi wani umarni ba daga mahukanta kan mayar da alawus din mambobin shirin zuwa Naira dubu 70.
"Wannan zancen ƙanzon kurege ne, wanda yayi hannun riga da gaskiya", inji sanarwar.
"Masu yiwa ƙasa hidima da iyaye da al'umma su sani babu wani umarni da aka samu daga gwamnati kan karin kudin. Don haka ba zai yiwu NYSC ta fitar da sanarwa kan hakan ba.
" Masu yiwa ƙasa hidima sun san hanyar da ake fitar da bayani daga shirin, don haka su yi watsi da batun karin kudin alwas"
Shirin na NYSC ya kuma shawarci masu yiwa kasa hidima da su kaucewa bibiyar shafukan dake yada irin wadannan bayanai.
managarciya