Gwamnatin Zamfara Ta yi kashedi Ga Hukumomin Gwamnati Da Kada Su Sake Magana Da Manema Labarai

Gwamnatin Zamfara Ta yi kashedi Ga Hukumomin Gwamnati Da Kada Su Sake Magana Da Manema Labarai

Daga Aminu Abudullahi Gusau.

Gwamnatin Jihar Zamfara ta hana jami’an ma’aikatu da hukumomin  ta bada bayanai dangane da manufofi da shirye-shiryen gwamnati ga manema labarai.

 Kwamishinan yada labarai na jihar Alhaji Ibrahim Dosara ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da mambobin kungiyar ‘yan jarida a Gusau babban birnin jiha.

 Dosara ya ce gwamnatin Zamfara ta sanya ma’aikatar kula da harkokin yada labarai ta bada bayanai ga duk dan jaridar dake son wani bayani wanda ya shafi gwamnati, domin dakile  yada labaran karya ga al’ummar Zamfara.

 “Wannan ya biyo bayan yanayin tsaro da ake fama da shi a jihar da kuma rashin bin ka'idar bada bayanai inda kowa ya dauki nasa ra’ayin kuma ya yi ta bakinsa a madadin gwamnati.

 “Hakan ya kara dagula al’amuran kalubalen tsaron da muke fama dashi a jihar, kuma majalisar zartarwar jihar na daya daga cikin kudurori da ta yi nazari a kanshi a taron ta na karshe da ta yanke shawarar karkatar da duk bayanan ta ga ma'aikatar yada labarai ta jiha.

 “Majalisar ta dauki matakin ne domin ta samu dama da kuma ikon dakile jerin labaran karya da ke  kara ta’azzara matsalar rashin tsaro a jihar.

 “Daga yanzu ma’aikatar yada labarai ko kwamishinan yada labarai ne kadai aka yarda ya yi magana a madadin gwamnati, yayin da mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin yada labarai, shi ne kadai aka yarda ya yi magana a madadin gwamnan.

 “Wayan nan mutane biyu masu kula da bayanan gwamnatin jihar Zamfara ne dangane da halin da ake ciki.

 “Muna kuma kira ga ‘yan jarida da su dauki wannan sauyin da aka samu  a matsayin aikin da zai  kawo masu sauki wajen samun bayanan da suke nema don rubuta rahotannin su.

 "Duk wata hukumar da ta yi magana da ku a madadin gwamnati idan ba kwamishinan yada labarai ko mai ba gwamna shawara kan harkokin yada labarai ba, wannan bayanin ba shi da amfani idan ya shafi gwamnatin jihar Zamfara," in ji Dosara.

 A wani bayani kuma, Gwamna Bello Matawalle ya amince da nadin Malam Musa Mailafiya a matsayin sabon Darakta Janar na wayar da kan jama’a, yada labarai da sadarwa na gidan gwamnati.

 Wannan yana kunshe ne  a wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar,  Kabiru Balarabe ya fitar, ya ce nadin ya fara aiki  nan take. Shi dai Musa Mailafiya ya maye gurbin Alhaji Yusuf Idris Gusau ne wanda ya samu sabon mukami na sakataren yada labarai na jam'iyyar APC a jihar ta Zamfara.