Rage karfin ikon Sarkin Musulmi:Gwamnatin Sakkwato za ta rika biyan albashi ga hakimman jihar
Kwamishinan lamurran kananan hukumomi da sarakuna Alhaji Ibraahim Adare ya ba da tabbacin in dokar da ke gaban majalisar dokokin jiha ta samu amincewa gwamnatin jiha za ta yanka albashi ga hakimmai domin tsamo su daga cikin wahalar da suke ciki.
Kwamishina Adare a wurin sauraren bahasin jama'a kan kudirin dokar a zauren majalisar dokokin jiha da aka gudanar a Talatar data gabata ya ce "in muka dubi kudirin dokar da aka gabatar a yau za mu fahimci lamarin a tarihi, uwayen kasa da hakimmai ana yin maganar su lokaci-lokaci ko a lokacin mulkin mallaka ana neman Gwamna domin ya bayar da amincewarsa wurin nada su, haka lamarin yake har lokacin mulkin soja, a lokacin mulkin Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa yana Gwamna aka daga darajar masarautar Sarkin Musulmi, a lokacin Sanata Aliyu Magatakarda aka canja tsarin aka baiwa majalisar Sarkin musulmi damar nada kananan hakimmai, haka lamarin ya zo har lokacin Sanata Aminu Waziri Tambuwal, a yau a wannan gwamnati ta Ahmad Aliyu aka fahimci akwai kurakurai nan da can aka ga ya dace a yi wa dokar gyaran fuska domin a daga darajar sarakanunan a addinance da al'adance da kuma tattalin arzikinsu.
"Za a yi hakan ne siba sa ga bukatar mutane domin sauyi yakan zo a kowane lokaci shi ne ya sa aka zo da wannan kudirin dokar.
"In ka dubi uwayen kasa da hakimmai ana son a daura su ne kan hanyar da dokar Nijeriya ta aminta ne domin a doka ba wanda yake da damar nada su sai majalisar zartarwa, ka ga kenan gwamna ke da wannan hurumin ko kuma wanda ya baiwa wannan damar a cikin 'yan majalisarsa, hakan ya sa aka kawo kudirin dokar domin 'yan majalisar dokoki su duba shi su kuma amince da mafi rinjayen jama'a da talakawa domin amfanar mutanenmu.
"Haka kuma in hakimmai gwamna yana da su dole ne ya kirkira masu albashi, a tarihi an san yanda hakimmai ke shan wahala musamman ba in za a biya su dan alawus da ake ba su, shugabannin kananan hukumomi sun san da haka, dan abin da ake ba su baya gamsar da su, ba ya biyan bukatunsu.
"Haka ma a gefen martabar su za ka darajar ta daga gwamna ne yake nada su, za ka ga kenan sun samu kusanci da gwamna da gwamnati, ita gwamnati za ta zama kusa da su, abin da kenan za a samu kulawa a kowane bangare, muna kira ga majalisa da mutane su aminta da wannan kudiri don inganata rayuwar mutane,"kalaman Kwamishinan kananan hukumomi.
managarciya