Ba ka da kimar sukar kowacce irin gwamnati - Fadar Shugaban Ƙasa ta mayar wa Obasanjo martani  

Ba ka da kimar sukar kowacce irin gwamnati - Fadar Shugaban Ƙasa ta mayar wa Obasanjo martani  

Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ba shi da hurumin ɗabi'a don suka Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, in ji Sunday Dare, Mai Ba da Shawara na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai ga Shugaban Ƙasa.  

Dare ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan maganganun da Obasanjo ya yi game da shugabancin Najeriya a wani shiri a Jami'ar Yale.  

A cikin jerin saƙonni a shafukan sada zumunta, Dare, wanda ya ce Obasanjo ba shi da gaskiya da hurumin ɗabi'a, ya ƙara da cewa ƙaryace-ƙaryacen sa sun yi fice a tarihi.  

Dare ya jaddada cewa zamanin mulkin Obasanjo ya kasance cike da cin hanci da rashawa, yana ambaton aikin wutar lantarki na dala biliyan 16 da aka yi wa caccaka sosai amma bai haifar da sakamako ba.  

"Tsohon Shugaban Ƙasa Obasanjo mutum ne mai ƙwarewa wajen shaci fadi, kuma 'yan Najeriya sun san hakan. Tafiyar sa kan hanyar ƙirƙirar surutan da ba gaskiya ba ,ta dade tana bayyana. Haka ma irin kuskuren da yake yi wajen juya gaskiya, yana mantawa cewa ya shugabanci gwamnatin da aka fi cin hanci da rashawa. Kalaman sa na baya-bayan nan a Jami'ar Yale sun rasa gaskiya,” in ji Dare.