Mai baiwa Gwamnan Sakkwato Shawara ya tallafawa magoya bayan APC da miliyan 22

Mai baiwa Gwamnan Sakkwato Shawara ya tallafawa magoya bayan APC da miliyan 22


Mai baiwa Gwamnan Sakkwato Dakta Ahmad Aliyu  Shawara kan samar da hanyoyin karkara Honarabul Malami Muhammad Galadanchi wanda aka fi sani da Bajare ya tallafawa magoya bayan jam'iyar APC a jiha da kudi miliyan 22 domin yin shagalin sallah karama.
Honarabul Bajare a wurin kaddamar da rabon a birnin jiha ranar Alhamis ya ce ya samar da wannan tallafin ne domin nuna godiyar sa ga damar da Jagoran tafiyar APC a Sakkwato Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko da Gwamnan Ahmad Aliyu suka ba shi don ba da tasa gudunmuwa ga cigaban jiha.
"Wannan tallafin na miliyan 22 mun samar da shi ne godiya ga jagororin mu, sako ne daga gare su zuwa gare ku da ba su amince mana ba da ba za mu yi ba, kuma a shirye muke mu yi sama da haka a duk sanda suka bukaci a yi.
"Mutanen ƙaramar hukumar Sakkwato ta Arewa sun cancanci godiya gare mu yanda suka sadaukar da kansu ganin jam'iyar APC ta yi nasara abin yabawa ne da yi masu kowace irin hidima."
Bajare ya ba da tabbacin cigaba da kyautatawa magoya bayan jam'iyar APC da Sanata Wamakko, lokaci bayan lokaci don ganin samun nasarar tafiyar su.
Ya yi fatar kammala shagalin sallah lafiya cikin lumana.
Honarabul Malami Bajare a rabon ya ce kalla mutanen da aka zakulo kowane zai amfana da dubu 100, wani 200 wani 300 har zuwa miliyan daya ya danganta da matakin da aka sanya ka.