2027: Magoya Bayan PDP Ne Za Su Yanke Shawarar Makomata----Atiku

2027: Magoya Bayan PDP Ne Za Su Yanke Shawarar Makomata----Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasar Nijeriya Alhaji Atiku Abubakar ya ce magoya bayan jam'iyar PDP ne za su yanke shawarar makomarsu kan babban zaɓen 2027 da zai zo.

Ya ce a yanzu an sauri sosai a yanke hukuncin kan ko zai shiga takarar shugaban ƙasa a babban zaɓe mai zuwa.

Atiku ya ce haduwar da Obi zai iya zama wata alama ce ta kokarin karfafa tafiya don tun karar babban zabe a 2027.