Ramadan: Miliyan 800 na ware domin tallafawa al’umma a watan azumi--Sanata Lamido

Ramadan: Miliyan 800 na ware domin tallafawa al’umma a watan azumi--Sanata Lamido

Sanata mai wakiltar yankin Sakkwato ta Gabas a majalisar dattijan Nijeriya  Sanata Ibramim Lamido ya ware miliyan 800 domin tallafawa al’ummar yankinsa a watan Ramadan in da za su amfana da tallafin abinci da sutura da kudi domin aiwatar da ibada cikin sauki da kwanciyar hankali.

Sanata Lamido a tattaunawarsa da manema labarai a Sakkwato a satin nan ya ce a wannan wata za a raba tirela 16 na abinci da kudinsu zai kai sama da naira miliyan 580 sama da mutum dubu 10 ne za su amfana da tallafin abincin.

"Wannan abincin  da zan raba 'yan siyasa za su amfana da masu lalura ta musamman da marayu da zawarawa da 'yan gudun hijira ba wani jinsin mutane da zamu bari baya. Haka ma na sayo sutura Atamfa da shadda da za a rabawa mutum dubu 22, zai yiwu ka samu shinkafa 'ya'yanka su samu shadda matanka su samu Atamfa wannan ne tsarin da muka yi a wannan watan na Ramadan na bana, mun yi haka ne domin Allah, ina fatan yin bayani ba zai sa lada ta rage ba," kalaman Sanata Lamido. 

  Wani abu da ya faranta ran mutanen jiha yadda aka baiwa mata da aka kashe mazajensu tallafin kudi, ya ce wadda ta rasa mijinta don ka ba ta dubu 200 ta yi sana'a ta dogara da kanta ba abin shela ba ne, su ne mutanen da yafi kamata a tausayawa a tunani na in kana da hali ka taimaki mabukaci sai Allah ya taimakeka, na yi haka ne don matan su iya kula da kansu da tarbiyar 'ya'yansu duk na samu dama zan cigaba da yin haka ba tare da kallon gefen siyasa ba domin dai jama'a su amfana Allah ya san da haka domin da zuciya yake aiki.

Da ya juya kan tsaro musamman kan zaratan mutanen da ya samar don tsare yankinsa ya ce "miye amfani na kwanta Abuja mutane na fama da matsalar tsaro suna kwana saman itace cikin tashin hankali ban yi Wani abu ba, samar da tsaro hakkinmu ne gaba daya ba sai shugaban kasa ko Gwamna ko Sanata kadai  ba, lamari ne al'umma ne gaba daya kowa ya ba da tasa gudunmuwa, anawa gefe ina yi ne tsakani da Allah don a samu nasara mutane su dawo cikin nutsuwa, taimakon Allah nake nema kan lamarin a karshe za mu yi nasara, gwamnatin tarayya da jiha dani dana jagoranci lamarin duk mun ba da gudunmwar samar da tsaro kamar yadda muka yi alkawali ga shi gwamnatin jiha ta kawo nata tsari nan gaba kadan zai kasance ba wani dan bindiga a yankin Sakkwato ta Gabas.