ANA BARIN HALAL.....:Fita Ta 41
ANA BARIN HALAL...
*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE*
*®️GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
_(Gaskiya Dokin Ƙarfe
Burin Mu Faɗakar Da Al’umma Domin Ribatar Duniya Da Lahira.)_
*BISMILLAHI RAHMANIR- RAHIM*
Idan kana/kina sha’awar:
_**Updates akan tallafin gwamnati (Grant & Loan)._
_**Hanyoyin samun kuɗi ta kasuwanci na online._
_**Sana’ar hannu da za ki iya yi daga gida._
_**Dabarun amfani da waya wajen samun kuɗi._
_To wannan group ɗin na Business/Grant/Loan naku ne! Zaku samu labarai kai tsaye + shawarwari masu amfani in sha Allah._
*Join yanzu don kada ku rasa sabbin damarmaki*
https://chat.whatsapp.com/C64wC3IDhW6FtwjSpWWDiL?mode=ac_t
*Page 41*
*INA UWARGIDAYEN SUKE? NACE INA UWARGIDAYE MASU CAPACITY SUKE, IDAN BAKI YI MATSA GA MASU* *AUTHOURITY, NACE TSAYA IDAN BAKIYI GA AMARE MASU AUTHOURITY,* *IDAN KIN SHIRYAH GWANGWAJE SHINFIƊAR MAIGIDA,* *TOU KI ƘYALE ƳAN LOCALLITY KI MATSO KI SAYI NAKI,* *BEDSHEETS ƳAN GASKE, KU MATSO KU YAƘI PORVERTY DAGA TASKAR HALIMA YISUF GWARZO, INA MAI TABBATAR MIKI IDAN KIN SHIMFIƊA ZAKI ZAMA MAI CAPACITY MAI AUTHOURITY,* *DOMIN KI WANKE ZUCIYAR MAIGIDA YA HASKAKA,*
*MUNA AIKAWA DA SHI KO'INA A FAƊIN ƘASAR NAN.*
*DOMIN SAYEN ƊAYA KO SARI, KU TUNTUƁE NI TA WANNAN LAMBAR*
08064586559
**********
Kwanci tashi asaran mai rai, duk abunda aka saka mishi lokaci saurin zuwa ne da shi, yau saura 3weeks bikin mu, daga gefen mun har nasu A.G da M.G shiri akeyi sosai, abun mamaki ƴan'uwan M.G da suka haɗa mahaifi tare, wato ƴaƴan Alkali sai shirin biki sukeyi babu kunya, Aunty umatiti har ashobi ta fito musu da shi wai na familyn su, da yake ita da Aunty safiya sunayi da shi sosai, don karatun ƴaƴan umatiti duk yana kanshi, shidai alƙawari yayi ƙafan shi bazai leƙa cikin gidan da aka wulaƙanta shi ba, amma komai ya kama idan baifi ƙarfin shi ba zai musu, gashi yadda Allah ya bunƙasa mishi dukiyan shi abun har abun mamaki.
Gidan mu kuwa zuwa wannan lokacin mamie hali ya fara dawowa, don sabeer ma fir ta mun hali akan ɗaukan shi, wai yanata laulayin haƙori, sbd haka abar shi jikn babu lafiya, haka ba a son raina ba na haƙura, amma kullum sai naje na duba shi, gashi da ƙiwuya, amma idan ya gani ya dinga wangale baki kenan yana dariya, hanani ɗaukan shi da tayi sai danayi ɗan ƙaramin zazzaɓi, sai da hajiya ummah ta watse ni tukun na haƙura wa raina.
Gyara sosai ake mun a side ɗin ummie, akwai wata ƙawar ummi mai suna hajiyan basakkwata, itama ta na unguwar mu na G.R.A, ita take mun gyara mai sunan shi gƴara.
A week ɗin aka kawo kayan aure gidan mu, kaya ne da ya amsa sunan shi kaya, set biyu na akwatuna A.G ya haɗa, M.G ma komai iri ɗaya aka yi, colour ne kawai yake banbanta, wai ranan zokiga mita a wurin mamie akan ba a gaya mata za'a kawo kaya ba, an maida ita meye a cikin gidan? Haka ta ringa bala'inta babu wanda ya kulata.
********
Gidan su Aliyu kuma haka Mummy tayi ta fama da shi har ya sake amincewa da auren ƴar sister ta, shima jamy ne ta nunawa Mummy abun da sukayi bai dace ba, itafa bataga laifin Ayshaa da iyaƴenta ba, saboda son da akeyiwa jammy ya saka mummy ta fahimceta, har ta ƙira ummie ta bata haƙuri.
Shirye-shirye mukeyi sosai na liyafa a ta gefen ummie, don zainab ta tattaro tun ana saura 2weeks ta dawo gidan mu, haka hadiza ma ana saura 1week ta dawo, kowan su itama an saka mata rana, kuma satin auren su yayah umar zasiyi passing-out, gashi ya matsa sai ummie taje mishi, mudai dariyan drammer su muke tasha, domin ita ta kafe saidai Aunty Rakiya idan zata tafi mamah ta bita, shi kua fir yaƙi yace shima ummie yake son gani a ranan, koyaya za'ayi Allah masani.
Yayuna sun mun akwatin kayan fitan biki, babu ne kawai babu a kayan, don gaskiya sun mun kaya na kece raini, ga furnitures ƴan gaske da aa mun Abuja da bauchi, kuma ko ina an saka mun gadaje, Abuja duka ɗakuna biyun Abba ya saka mun gadaje, bauchi kuma sise ɗina ɗaki ɗaya ne ba'a saka ba, gado uku su yayah suka mun, ɗaya aka kai side ɗin A.G, ranan da akaje akayi jere shima an sha daga da mamie dn har da kukanta, akan ana mata rashin adalci, Abba dai kacha-kacha ya mata ya barta, dayake ana gobe passing-out ɗin su yayah su Aunty J Da Aunty B suka haɗu da Adda da Aunty ma'u da ta sauƙa Abujan sukayi, kuma ranan su ummie suka sauƙa Abujan, da yake mamah tana Abuja lokacin tare da Abba, tou duk tare sukaje wurin bikin fitan su Yayah, ga hafsy da ummitah ansha sabbin ɗinkuna taya masoyan su murna duk sunje, mu da su hadiza da Maryam da Goggonta aka bari a gida, sai mamie da take gefenta ita da raliya da tazo ranan da su ummie suka tafi, tayi wani kyau daga gani tana hutawa, sai dai bangan alaman taa da ciki ba, don naga daga Fatima har maryam suna da ciki, don maryam lokacin ma tana kwance cikin laulayi sosai, don sai da mukaje muka duba ta ana gobe su ummie zasu tafi, don a gidan suka ɗauki ummitah ma da zasu tafi, duk tayi wani iri abun tausayi.
A.G ma ranan suka shigo bauchi shidah M.G, don sun baro masu jere sunje, zuwa dare ko ya iso gidan mu, parlon hajita ummah muka zauna, hadiza da maryam sunzo sun gaisa, da yake hadiza ƴar barkwanci ce ta saka shi a gaba da zolaya babu yadda ya iya dole ya amsa mata, ita dai zainab ƴar shiru ce daga gaisuwan ma wucewa tayi ɗakin hajiya ummah, don idan baka fahimce ta bafa zaka ɗauka mugun halinta ya kai inda ba'a zato,, koni da muna yara haushinta nake ji, don idan tazo gidan mu tayita haɗa rai wa habiba, shiyasa na tsaneta, don wataran ni ko bin ta kanta banayi har tayi kwanakinta ta tafi, sai yanzu nake ɗan fahimtan wasu halayenta, ita ba mai son hayaniya ba ce, sannan kuma ba kuwa hankalinta yake ɗauka ba, idan baka mata tou ko za'ayi yaya da ita bata bin ta kanka, abunda na lura kuma ƴan'uwan ummie suna jin haushin abunda mamie take yi mata, shiya jawo bata son habiba ko kaɗan.
Itama hadiza tashi tayi ta bar mu nida A.G, kallo na namayar kanshi lokacin da ta wuce ɗaki wurin su zainab, gira ya ɗaga mun duka biyu yace, "meye sirrin wannan ƙamshi da kyau da kikayi Eeshaa? Sai wani zabura nakeyi ni kaɗai, Allah ma ya taimaka su hadiza sun zauna, anya zan sake dawowa kuwa"? Ya faɗa yana kashe mun idon shi na jaraban nan, tura baki nayi gaba cike da shagwaɓa nace, "haka ma fah akeyi, har sai ranan auren fah ya kamata ka ganni".
Tasowa yayi ya dawo kueran da yafi kusa dani ya zauna, ya buɗe baki zaiyi magana mukaga an ɗago labulen parlon, namie ce ta shigo, zuciyata naji yayi wani mumunan yankewa, gashi wani kallo ta bi A.G da shi sannan ta dawo da idonta kaina, "amma saboda Allah ayshaa har an shiga satin aurenki baki taɓa tunani ko ke ko mamanki ba ku saka mai auren ki yazo ya gaishe ni ba? Ko don ni Allah ya ɗauke tawa ƴar kuke nuna mun haka? A hakan kike zaton na baku riƙon sabeer bayan mai riƙewan bai san girma na ba"? Da sauri A.G yafara gaisheta, rai a ɓace ta amsa mishi, ni dai bance komai ba na sunkuyar da kaina ƙasa ina mamakin ta a zuciyata.
Hummm ta furta bayan ta nemi wuri wa kanta ta zauna, hankalinta ta mayar kan A.G, "kasan tun suna yara mahaifiyarta ta hanata raɓa na, gashi Allah ya haɗa tsakaninta da habiba ƴar wurina, tou meƴe aciki idan sunyi zumuncin su da Allah ya haɗa su na mahaifi ɗaya? Sai muyi namu kishin daban mu bar yara suyi zumuncin su, amma da yake ana ganin ni bani da haƙuri ina faɗin gaskiya sai duk kowa yaƙi jinina a gidan nan, tou gashi dai wacce ake husumar yanzu bata raye, basai a bar komai ya wuce ba, ae dai ko sau ɗaya za'ace kazo ka gaishe ni," ta faɗa tana share hawayen fuskanta, duk nidai jikina sai rawa yakeyi na abun da tayi, mamaki ne ko tsoro ta bani ohoo, "don Allah kiyi haƙuri, insha Allahu zamu gyara, zamuzo nida ɗan'uwana na musamman mu gaisheki, ita kuma ayshaa zata gyara na miki alƙawari", A.G ya faɗa yana wani risina mata, haka ta miƙe ta fice tana, "Allah yasa su barka, don ni bansan faɗin gaskiya yana saka kayi baƙin jini ba".
Ido ya ƙura mun yana murmushi, ganin duk fuskana ya chanja yasaka yace, "me kuma ya faru? Gaskiya ta faɗa ae beauty, yaka mata ko sau ɗaya kice muje mu gaisheta ae, tuda ita mamah muna gaisheta a chan Abuja, amma ba komai na miki uzuri ke yarinya ce ay be bakiyi tunanin ayi haka ba, insha Allahu zamu gyara", ya faɗa yana kallona cike da murmushi.
Ajiyan zuciya na sauƙe ina cike da mamakin mamie, bance mishi komai ba kada ya ga mune da gaske bamu son a zauna lafiya, tunda shidah ba sani zaiyi ba, haka dai muka gama hiran ya tafi, koda ya tafi ban gayawa su Hadiza ba , gudun kada suyi magana hajiya ummah ta samu mamie, daga nan kuma ban san me zata zo tagaya mishi ba, haka dai na bar komai a zuciyata nayi shiru.
Ranan da su ummie na suka dawo, bataliya guda suka dawo, son har dasu ƴan'uwa na da matan su, da gudu na fita naje na rungume yayah umar, duk sai naga ya zama wani ƙato da shi, dama yafi su yayah muhammad siffan girman jiki, dariya yakeyi yana ta wani juyawa da ni, nima dariyan nakeyi nace, "yayah congratulation, Allah yasa kungama a sa'a", Ameen kowa ya amsa har da shi da yake cike da farin cikin ganina, "sisto na gama na dawo ke kuma zaki gudu ki bar ni da mai rusheshen kan nan"? Ya faɗa yana dariya, kowa yasan da hafsy yakeyi sai yayah muhammad yace, "mudai babu ruwan mu kunfi kusa kai da mai rusheshen kan", ya faɗa yana miƙa mun hannun shi, wurin shi naje na rungume shi ina "oyoyoyo best broh" shima oyoyon yayi mun, inda nabi su 1 by 1 Ina musu oyoyoyo, daga yayuna har matayen shu, su ummie dama sun wuce ciki da su goggo, Aunty Ruƙayyah da Aunty ma'u sun wuce tare da yayah ishaq, akan zuwa dare zasu shigo, gida dai ya cika sosai, nan suke cewa gobe Abba da mamah zasu taho insha Allahu, flight zasu biyo, nidai murna da daɗi nakeji a zuciyata, nan su Zainab da hadiza suayi wa yayah umar murna, hannu ya miƙa musu suka tafa, yana tsukanan zainab, "dunkum ae ina ta Allah- Allah kizo ko soja zasu ɗauke ki sunga irin su", dariya aka yi ita kuma tana hararan shi tace, "ina zuwa sallaman ka zasuyi suce wannan maganannen sojan a sallame shi a ɗauki asalin sojar", haka dai akaita raha, hadiza ta taya goggo jera musu abinci, nidai dama Goggo ta hanani komai a gidan iyakata naci nayi wanka a mun gyara.
Yayah Ahmad ne ya ƙura mun ido, "kai matar barrister wannan shinning ɗin da kike tayi ya kamata barrister fah ya ƙara sadaki, don 2million zan karɓa", ya faɗa cike da zolaya, "amma yayah ae karage mata, irin kyaun nan da tayi ae gida da mota zai ƙara", yayah umar ya faɗa shima da zolayan, nidai na tura baki gaba ina kallon yayah muhammad cike da shagwaɓa, hannu ya miƙo mun yace, "rabu da su bestyn besty, zo muyi wani ƙus-ƙus ɗin mu ni dake", matsawa nayi dab da shi na zauna ina hararan marenin wayo na, shi kuma yana kai loman abinci yana wani kaɗa mun kai irin alaman zai haɗu dani.
Ƙus-ƙus ɗinmu mukayi nida yayah na, duk yadda yayah Ahmad yake turo kai su Adda dasu Aunty J suna mishi dariya bai ji mu ba, chan kuma wayan shi ta fara ƙara, "wannan jarababben mijin naki ya dameni da nazo, nifa ya kama kanshi ni yanzu ba abokin shi bane yayan shine", ya faɗa yana ɗaga wayan, ido muka zuba mishi nida yayah muhammad, fuskan yayah muhammad ɗauke da murmushi, "barrister yyh ake cike ne? Ka matsa mun fa bayan madam ta hanani fita", baki Aunty J ta riƙe tana zare ido, shi kuma dariya yayi yace, "tou basai na saka a ɗaga ɗaurin auren ba, kasan nine alwali, wancan yayah m ne yayi na marigayiya, ni ko don ka kama kanka ma zancwwa Abba don Allah abani", bamuji me A.G ya faɗa ba amma ganin dariyan da Yaya Ahmad yake bayan dariya ba al'adan shi bane yasaka kowa ma ya dara, nidai sum-sum na tashi na bar wajen, jin yayah Ahmad nace mishi bazai bashi ba idan bai ƙara sadaki ba, ko me A.G yace naji Yaya Ahmad nacewa "tou ka taimaki kanks, ina ɗaya sususaccan angon"? Banji yayah suka ƙare ba na wuce chan ɗakin mu, anan na samu Aunty B kwance, don hafsy na tare da Areef a ɗakin ummie.
Ranan da sukaje jere washe garin da wowan su ranan su Abba suka dawo da mamah, babu wanda ya aiki mamie ta wani je gidan jere, bata daɗe ba ta dawo da wannan bala'in, nan Abba yayi mata kacha-kacha, ganin idon yayah umar da yayah ishaq ne ma da suka fito ya saka ta koma side ɗin ta , amma inaga taso abun yafi haka, don babu rahma a tattare da ita, kusan dab magreeb Mummyn Aliyu suka shigo ita da ƙawarta, gudumawa sosai na wasu manyan bedsheets guda biyu ta kawo masu kyaun gaske, tura hafsy tayi a ɗauko mata sabeer ta ganshi, amma fir mamie ta hana, koda aka zo aka gaya mata bata ce uffan ba bayan murmushi da tayi, hira suka cigaba dayi basu bi takan mamie ba, har akayi sallan isha sai ga yayah umar ya shigo, cike da isa da iya bariki mummy ta kalle shi, "yauwa ɗana soja, nace ko zaka taimaka ka kawo mun ɗanku na wurin Aliyu na ɗan ganshi"? Cike da gadara yayah umar yaje ya amso shi kuwa, kar ɓan shi tayi ra kalle shi daga nan ta mishi addu'a ta miƙawa ƙawarta, pics sosai suka mishi sannan suka yi sallama da ummie suka miƙawa hafsy akan ta maida shi.
Basu daɗe da tafiya ba hafsy ta shigo baki a zunɓure, kallonta ummie tayi ta ɗaga kanta, goggo ce ta tambayeta me ya faru? Bako a ture a gaba tace, "wannan matar da ƴarta wallahi ƴan rainin wayo ne, tsabar ni ta rainani bani na karɓo yaron ba ina maida shi ta wani rufeni da zagi tana zagin ummien mu, wallahi darajan Abba taci yau dana gaya mata maganan da har ta mutu bazata manta ba,"
"kul naji wannan ranan, babu ruwanki da su", ummie ta faɗa, "tou ummie ta isa tayiwa yayah umar ne? Itama raliya har da tsoma ruɓaɓɓen bakinta wai, ko wani abu akayiwa yaron da aka ɗauke shi? Allah ya kare musu yaro, " hafsy ta faɗa ta na wani cika kaman zata fashe.
"Baki naushi bakin marar kunya ba"? Zainab ta tambayi hafsy, ita dai hafsy na kallon ummie tace, "na ajiye mata kykkyawan warning, idan ta sake shiga sabgata kafin ta tafi zan zane ta, ina faɗa na fito na barsu da baƙin ciki", ta faɗa tana juya ido
"Allah ya kyauta, ki zaneta kiga matakin da mijinta zai ɗauka akanki" ummie ta faɗa, dariya hadiza ta saka tace "haba ummie ita mai miji soja har za'a gaya mata ɗaukan mataki"? Dariya hafsy ta kece da shi tana, "gaya musu dai Adda hadiza, yanzu yayah ishaq yasaka yarinyar da mijinta tsallen kwaɗo wlh".
Har ummie dariya muka saka, wallah hafsy bata kunyar hiran yayah ishaq da ummie, don har ƙiranshi mijinta takeyi a gaban ummie, nikan bazan iya ba kunya nake ji Aunty nice.
Murmushi nayi ina kallon hajiya Ayshaa, hannu ta miƙa ta ɗauki goran ruwa tasha kaɗan, sannan ta cigaba.
Sai da naga duk sun fita tukun na gayawa ummie abunda mamie taje ta mun a gaban A.G, ido ummie ta ƙura mun, har wani lokaci tukun tace, "tou meye nufinta da zuwa wurin shi? Kuma me takeso yayi mata idan yaje gaisheta? Tou aniyarta ta bita, bazai je ba, kada ki yadda ki kulata balle ki kaishi", haka mukai ta hiran mu da ummie tana ɗan ƙara mun haske a rayuwa da kuma kula da mutane.
Su Aunty j duk sun wuce gidajen su tun magrib da mazajen su, ummie tace kowa taje ta huta, A.G bai sake shigiwa gidan mu ba don sanin a cike yake da mutane, amma waya kam har mamakin yawan ƙiran da yake yi nakeyi, a haka ranan alhamis aka zo aka zizara mun lalle da kitso, tun daga maiduguri Aunty Bintu ta saka fatima su taho da mai lallen, wednesday suka zo, fatima da ɗan ƙaramin cikinta wanda yayi mata kyau cif da ita, ba irin na maryam ba da yake wahalar da ita sosai, fatima da kitsonta da lallenta tazo, saboda haka washegari ni dasu hadiza da su hafsy mukayi, sai wasu feiends ɗinmu da muka haɗu da su a A.T.B.U da suka zo, babu kunya da yamma raliya ta aiko wai mai lallen idan tagama don Allah tazo ta mata, hararan ƴar aikan zainab tayi, "kice bata da wannan kuɗin da zata mana iko irin haka, ta nema a ɗauko mata wata daban", ƴar aikan tana fita hafsy ta sheƙe da dariya tace, "sai Adda jebo, ae da gangan ana gama yi mun na wuce side ɗin su, tana gani ta wani taso tana rangwaɗa wai don Allah hafsy ina kika samu aka miki wannan haɗaɗɗen lallen? Shine nagaya mata from maiduguri Aunty B ta ɗauko mana mai yi, har da kitso wa amaryah, shine wai ae bata sani ba ko itagama zata zo ta mata, wai wallahi mijinta yana son lalle da kitso fa, nidai na isar da abinda ya mun na fito na barta, shine hakima bari ta aiko? Tou ta haɗu da Adda jebo yau".
Dukkan mu ɗakin dariya muka saka, don gaskiya hagsy tsiyarta yana da yawa, ita kanta mai lallen dariya take yi.
Ana gama cire mun na koma gefe na ɗauki wayan A.G, duk da nace mishi lalle fah ake mun amma bai fasa ƙira akai akai ba, ima ɗauka kuwa ya wani ajiye ajiyan zuciya, "Beauty", kawai iya abunda ya faɗa yayi shiru, murmishi nayi don nasan me yake nufi, ya gama gajjiya da galabaitan rashin jina yau, saboda yanzu maganan shi ɗaya nasan me yake nufi, idon shi ma idan na duba nasan meye yake so, "sai yanzu aka gama ne fah", na gaɗa mishi don ya kwantar da hankalin shi, "ina son ganinki", zaro ido nayi kaman yana ganina nace, "amma kasan gidan fah acike yake, yayah za'ayi ka shigo? Bakajin kunya ne"? Ajiyan zuciyan shi na sake ji mai ɗan ƙarfi, da kuma jin sautin numfashin shi kaman babu lafiya, a hankali nace. "kasha magani? Ko kasha wani abu mai sanyi ne"? "Eeshaa ni ke nake son gani", ya sake faɗa yana jan numfashin a hankali, duk sai naji babu daɗi amma ni bansan yayah zanyi ba, shiru nayi ina sauraron numfashin shi da yake fita da wani irn sauti, "Beauty", ina jin shi amma nakasa amsa mishi, shima daga nan shiru ya sakeyi, "zanzo" ajiyan zuciya nayi sanan nace, "Allah ya kawo ka lpy, ka kula da kanka".
Daga nan muka ajiye wayan, amma duk sai najini babu wani kuzari a tare dani.
Ina idaar da sallan magrib na shige kitchen ɗin ummie na ɗaura tea mai haɗe da kayan maiduguri na ƙamshi, bayan na tafasa na jure a flask ƙarami, sannan na ɗebi cake na saka a takeaway na wuce ɗakin mu da shi, kan mirrow na ajiye na shige wanka.
*AUNTY NICE
managarciya