An ɗaura auren ƴar sarkin Bichi da ɗan shugaban Najeriya, Yusuf Buhari da Zahra Bayero

An ɗaura auren ƴar sarkin Bichi da ɗan shugaban Najeriya, Yusuf Buhari da Zahra Bayero
An ɗaura auren ƴar sarkin Bichi da ɗan shugaban Najeriya, Yusuf Buhari da Zahra Bayero
Daga Comr Aliyu Abdul Garo.
An ɗaura auren Yusuf Muhammadu Buhari da Zahra Nasir Bayero a Yau juma'a a babban masallacin garin Bichi kan sadaki naira 500,000.
Inda Alhaji Aminu Dantata ne waliyyin amarya yayin da Malam Mamman Daura ne waliyyin ango. Ministan Sadarwa Malam Isa Ali Pantami ne ya daura auren na Yusuf da Zahra, An ɗaura auren ne da misalin ƙarfe 2:38 na ranar Juma'a.
Inda Manyan jami'an gwamnati da ƴan siyasa wandan da suka haɗa da gwamnoni, da sanatoci, da ƴan majalisa tarayya, ministoci da dai saurensu, inda aka tsaurara tsaro a gidan Sarkin Bichi da kuma masallacin Bichi, inda a nan ne aka daura auren Yusuf, ɗan Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Zahra, ƴar Sarkin Bichi Nasiru Ado Bayero, a yau.
Jami'an tsaron fadar shugaban ƙasa ne ke kula da al'amuran tsaro a gidan Sarkin na Bichi da kuma masallacin da aka gudanar da ɗaurin auren, Sannan tun daga cikin birnin Kano har zuwa Bichi an ajiye jami'an tsaro na soja da ƴan sanda a kan tituna, wandan da suka hada da Sojoji da ƴan sanda da jami'an farin kaya na DSS su ne suka fi yawa sai dai akwai na Civil Defence da kuma Road Safety.