Gwamna Zulum Ya Tsawaita Shekarun Ritayar Malaman Borno Zuwa Shekaru 65
Daga Sani Saleh Chinade, Damaturu.
Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya amince da tsawaita shekarun ritayar malamai daga shekaru 60 zuwa 65 a jihar.
Gwamnan ya sanar da hakan ne a domin tunawa da ranar malamai ta duniya ta shekerar 2022 da aka gudanar a garin Maiduguri.
Kwamishinan Ilimi na Jihar Borno, Injiniya Lawan Abba Wakilbe, shi ne ya wakilci gwamnan a wajen bikin na bana wanda aka yi wa taken: “Canjin Ilimi Ya Fara Da Malamai”.
Zulum ya bayyana cewa tuni ofishin sa ya rubutawa majalisar dokokin jihar Borno yana neman a kafa dokar da za ta goyi bayan tsawaita wa’adin aikin malamai daga shekaru 35 zuwa 40 da kuma ritaya daga shekaru 60 zuwa 65.
Gwamnan ya kuma bayyana sake fasalin kwamitin daukaka kara da aka kafa a baya, tare da sabon wa'adin duba ikirari da wasu malaman da aka kora a yayin wani aikin tantancewa da kwamitoci suka yi kan batutuwan da suka shafi malaman bogi, da kuma rashin cancantar da ake bukata, da dai sauransu. .
An bukaci kwamitin da ya sake duba cancantar ikirarin malaman da abin ya shafa don tantance wadanda suka cancanci sake shiga aikin koyarwa.
Gwamnan ya kuma yi alkawarin duba wuraren da aka samu baraka a dokokin Ilimi na Jihar domin ya shafi jin dadin malamai da kuma yadda wasu dokokin tarayya ke amfani da su a jihar Borno.
Cikin farin ciki da manufofin Gwamna Zulum da ke inganta jin dadin mambobinta, kungiyar malamai ta Najeriya (NUT), reshen jihar Borno, ta sanar da kyautar NUT ta musamman ga Farfesa Zulum don nuna godiya.
Shugaban kungiyar NUT a jihar, Kwamared Jibrin Mohammed, wanda ya bayyana hakan a yayin bikin ranar malamai ta duniya, ya ce an yi karramawar ne domin kaan abubuwan da Farfesa Zulum ya yi na inganta jin dadin malamai a fadin jihar.
Shugaban kungiyar ya bayyana cewa kungiyar na fatan bayar da wannan lambar yabo a ranar 28 ga watan Nuwamba, 2022, a taron wakilan NUT da aka shirya gudanarwa a Maiduguri.
Shima da yake jawabi a wajen taron, shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya NLC a jihar Borno, Kwamared Inuwa Yusuf, ya yabawa gwamnatin Gwamna Zulum bisa inganta jin dadin ma’aikata.
Sai dai ya roki gwamnati da ta sake shirya wani zagaye na horaswa ga malamai sama da 7000 da aka ware domin kara samun horo.
A nasa bangaren, Shugaban Hukumar Ilimi ta bai daya ta Jihar Borno (SUBEB), Farfesa Bulama Kagu, ya bukaci malamai su kara himma wajen aiki.
Babban abin da ya fi daukar hankali a wajen bikin shi ne bayar da lambar yabo ta NUT ga Kwamishinan Ilimi na Jihar Borno da kuma Provost na Kwalejin Ilimi ta Sir Kashim Maiduguri, Dokta Abba Mala, bisa ga bajintar ayyukan da suka yi a matsayinsu na masu rike da mukaman gwamnati.
managarciya