An tsinci gawar ɗansanda a otel a jihar Ogun
An tsinci gawar wani ɗansanda mai muƙamin sifeto, mai suna Haruna Mohammed a dakin wani otel a jihar Ogun.
Daily Trust ta tattaro cewa, ɗansandan da ke aiki a caji-ofis na Ishashi a jihar Legas, ya je otal din mai suna Super G Royal, da ke Anthony Uzum Estate, Oyeyemi Akute shi da wata mata da misalin karfe 1:00 na dare a ranar Asabar.
Rahotanni sun ce manajan otal din, Deborah Adejobi, ta iske dakin nasu a bude da misalin karfe 8:52 na safe, inda ta leka ciki, ta gano ɗansandan a kwance ba ya motsi kuma ba a ga matar ba.
Daily Trust ta ce a bayanin da rundunar ƴansanda ta fitar da ke bayyana rahoton halin da ake ciki, mai otal din, Abiodun Olagunju ne ya kai rahoton faruwar lamarin ga rundunar, inda ya kara da cewa matar, wacce tuni ta tsere, ta zo ta sayi ruwan sha a wajen karɓar baƙi na ital din da misalin karfe 6:00 na safe.
Tuni dai a dauke gawar kuma aka ajiye ta a mutuwarsa ta asibitin Life Channel da ke a Olambe.
Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin Rundunar ƴansandan Jihar Ogun, Omolola Odutola, ya ce: “Da farko dai an ga kakin ƴansanda a cikin jakarsa ce, don haka ba lallai ma a ce shi dansanda ne ba. Babu katin shaida a kansa ko kayansa," in ji shi.
managarciya