An Kwashe Dukkan 'Yan Nijeriya Dake Sudan---Gwamnatin Tarayya

An Kwashe Dukkan 'Yan Nijeriya Dake Sudan---Gwamnatin Tarayya

 

Gwamnatin tarayyar Nijeriya a jiya ta kwashe dukkan 'yan ƙasar ta dake zaune a Sudan dake buƙatar su dawo kan matsalar yaki da ake yi a ƙasar.

Gwamantin ta tabbatar ba wata rayuwa da ta salwanta a wirin kwasar mutanen sai dai akwai ɗalibai 92 da suka maƙale a can saboda gwamnatin ƙasar ta ƙi aminta a dawo da su.
A bayanin da ma'aikatar harkokin ƙasashen waje da agajin gaggawa sun tabbatar da an kwashe mutane ba a bar kowa ba.