'Yan Jaridar  Zamfara suna cikin hadari bayan 'Yan Bangar Siyasa sun daki Shugabansu, sun yi masu barazana

'Yan Jaridar  Zamfara suna cikin hadari bayan 'Yan Bangar Siyasa sun daki Shugabansu, sun yi masu barazana
 
Daga Hussaini Ibrahim, Gusau
 
A yau Alhamis dinnna  ne wasu ‘yan Bangar Siyasa suka lakada wa Shugaban kungiyar ‘yan jarida NUJ reshen jihar Zamfara. Sakamakon dakatar da aikin ginin shagon mallakar NUJ ,da su 'Yan Bangar keyi .
 
’Yan Bangar Siyasa sun yi kaca-kaca ne bayan shugaban kungiyar Kwamared Ibrahim Musa Maizare ya nemi dakatar da aikin shagunan NUJ da su 'Yan Bangar Siyasa keyi da sunan wani Babban Dan Siyasa ne ya ba su damar cigaba da aikin shagon da ke mallakar kungiyar ta NUJ.
 
‘Yan Bangar sun ce ba za su daina aikin ba ko kuma su bar wurin saboda wani Babban  Dan siyasa ne ya ba su kuma a yayin da wannan dan siyasar ke numfashi ba za su taba barin wurin ba.
 
Tun da farko an dauki shago na NUJ a matsayin gidan cin abinci amma bayan dan hayar ya daina kasuwancin gidan abincin ya bar wajen sai ‘yan bangan suka mayar da shi ofishin yakin neman zabe.
 
Shagon 'Yan Bangar Siyasa sun kone shi ne  a shekarar 2021 kuma kungiyar ta NUJ ta bukaci ‘yan bangar da su bar ofishin saboda fargabar jefa daukacin shagunan NUJ da sauran shagunan da ke cikinsa cikin hadari.amma abun yaci tura .
 
Sakamakon Koken da Kungiyar NUJ ta ke ma Rudunar 'Yan sanda rahotan abunda ke faruwa , tawagar ‘yan sanda ta isa Sakatariyar NUJ, ‘yan Bangar sun ci gaba da zagin jami’ai da sauran mambobin kungiyar. 'Yan Jaridu  suna zagunsu da barazanar halaka duk Wanda ya ce baza su zauna a shagon ba,agaban 'Yan sanda suka ta wannnan furuncin kisan 'Yan Jaridun. 
 
Da yake jawabi ga manema labarai jim kadan bayan faruwar lamarin, Sakataren kungiyar Ibrahim Ahmad Gada ya bukaci hukumomin tsaro da su kare rayuka da dukiyoyin ‘yan jarida, ya kara da cewa ,rayukan ‘yan jarida masu aiki a jihar na cikin hadari matuka.
 
"Idan dan daba ya iya yin barazanar kashe 'yan jarida masu aiki me kuke tsammani. Dole ne a tabbatar da tsaron dukkan 'yan jaridan da ke aiki a fadin jihar ta zamfara .
 
Sakataren yayi kira ga masu ruwa da tsaki da su shiga tsakani, da Gwamnatin da kungiyoyi masu zaman kansu Dan kare rayukan 'yan Jaridu da dukiyoyin su " in ji Gada.