An Kai  Jaruma Hafsa Idris Ƙara Kotu Don  Ta Biya Wasu Maƙudan Kudi Da Ta Cinye

Jarummai mata a masana'anyar shirya finafinnai ta Kannywood sun shahara ga wannan ɗabi'ar ta riƙe kuɗin mashirya finafinnai ba tare da gudanar da aikin da aka ba su ba.

An Kai  Jaruma Hafsa Idris Ƙara Kotu Don  Ta Biya Wasu Maƙudan Kudi Da Ta Cinye
Hafsat Idris
Wani rahoto da gidan Radio Dala FM dake Kano ya kawo ya bayyana cewa wani kamfanin shirya finafinnai  ya kai ƙarar jarumar Kannywood Hafsat Idris wacce aka fi sani da Barauniya,  gaban babbar kotun jihar Kano, wacce ke Ungoggo, kan zargin cinye zunzurutun kuɗi har naira miliyan daya da dubu dari uku da aka bata domin daukar bidiyon rawa, amma ta saɓa alkawari.
Rahoton ya bayyana cewa jarumar ta zo gurin bikin, har an fara daukar bidiyon, sai kuma ta gudu ba ta dawo ba, inda hakan yasa kamfanin ke buƙatar kotu ta sa ta dawo musu da kuɗin su, kana ta biya su naira miliyan goma.
Sun bukaci wannan naira miliyan goma ne a matsayin diiyyar asarar da ta sa suka yi domin sun tara ma’aikata sun ɗauko hayar kayan aiki, sai kuma rashin cika alƙawarinta yasa sun yi asara.
Har ya zuwa yanzu dai ba a  ji ta bakin ita jaruma Hafsat Idris kan wannan batun ba.
Jarummai mata a masana'anyar shirya finafinnai ta Kannywood sun shahara ga wannan ɗabi'ar ta riƙe kuɗin mashirya finafinnai ba tare da gudanar da aikin da aka ba su ba.