Jirgin Yaƙi Ya Yi Luguden Wuta Ga Mahara A Sakkwato Da Katsina

A daya daga cikin hare-haren, jiragen yakin sun lalata sansanin wani dan ta’adda da ake kira ‘Gajere’ inda aka kashe yaransa 34, wasu kusan 20 kuma sun samu raunukan harbi

Jirgin Yaƙi Ya Yi Luguden Wuta Ga Mahara A Sakkwato Da Katsina
Jirgin yaƙin sojan Saman Nijeriya ya yi luguden wuta ga mahara a jihar Sakkwato da Katsina.
 
A daya daga cikin hare-haren, jiragen yakin sun lalata sansanin wani dan ta’adda da ake kira ‘Gajere’ inda aka kashe yaransa 34, wasu kusan 20 kuma sun samu raunukan harbi.
A Jihar Sakkwato dakarun sojin karkashin rundunar ‘Hadarin Daji’ sun kai hare-hare ne ta sama a dazukan Mashema, Yanfako, Gebe da kuma Gatawa a kananan hukumomin Isa da Sabon Birni.
Wata majiya ta soji  ta bayyana cewa an samu nasarar hakan ne a ruwan bama-bamai da suka yi ranar 5 ga watan Oktoba 2021, bayan sintirin da aka yi ta yi ta sama wanda ya gano wuraren da ’yan bindigar ke boyewa a cikin dazukan.

Rahotanni sun ruwaito mutanen da ke zaune a yankunan da aka kai hare-haren suna bayar da labarin yadda suka ga maharan na ta tserewa, yayin da wasu suka fake a wata makarantar firamare da ke kauyen Bafarawa.

A Jihar Katsina an gano yadda jiragen yakin Najeriya suka yi ta ruwan bama-bamai a maboyar maharan a dajin Rugu da ke da iyaka da Karamar Hukumar Kankara ta Jihar Katsina a tsakanin ranar 30 ga watan Satumba da 3 ga watan Oktoba, 2021.

Wannan farmakin na Sojan Nijeriya yana faranta ran mutanen ƙasa ganinn yanda mahara suka addabi yankunan da ke fama da tashin hankali.
Luguden wutar abu ne da ake sa ran a cigaba da shi har a kawo ƙarshe maharan.