Akwai Bukatar Al'ummar Hausawa Su Daina  Kallon Finafinnan Hausa---Jami'ar Usman Danfodiyo

Akwai Bukatar Al'ummar Hausawa Su Daina  Kallon Finafinnan Hausa---Jami'ar Usman Danfodiyo

 

 

Jami'ar Usman Danfodiyo dake Sakkwato ta yi taron yini daya da masana a kan finafinnan Hausa da zamantakwar magidanta: Ina aka Dosa?

A bayanin bayar taro da aka fitar wanda shugaban kwamitin taron Farfesa Yakubu A. Gobir da shugaban sashen koyar da Harsunn Nijeriya Farfesa B.B Usman suka sanyawa hannu sun ce masana sun bayar da shawarwari masu yawa kan batun da aka tattauna.

An bayar da shawarwari guda biyaar domin dawo da al'umma cikin tsari mai kyau, "akwai bukatar a rika shirya finafinnan Hausa wadanda suke nuna darussan kyawawan al'adun zamantakewar auren Hausawa na tarbiyya da kunya da biyayya tsakanin ma'aurata da 'ya'yansu kamar yadda wasannin kwaikwayo na da suka nuna.

"Akwai bukatar magidanta da sauran al'ummar Hausawa su kauce wa kallon finafinnan Hausa na wannan zamanai wadanda suka saba wa al'adu da addini da tarbiyar Hausawa, wannan zai rage yaduwar finafinnan da amfani da miyagun darussan da ke cikinsu. 

"Al'ummar Hausawa(musamman matan aure) su guji dogewa da bata lokaci wajen kallon finafinnan Hausa da amfani da miyagun darussa da ke cikin na amfani da miyagun kalamai da saka sutura wadanda suka sabawa al'adun Hausawa da ke haddasa matsalolin rashin jituwa tsakanin ma'aurata da mutuwar aure barkatai.

"Ana ba da shawarar masana da manazarta su mayar da hankali sosai wajen rubutawa da shirya finafinnai Hausa masu koyar da kyawawan al'adu da dabi'un Hausawa. Gwamnati kuwa ta tallafa wajen daukar nauyin samar da da yada su."

A karshen taron shugaban jam'iar Farfesa Lawal Sulaiman Bilbis ya yi  godiya ga mahalarta taron da wadanda suka bayar da gudunmuwa, ya kuma alkawalin za a ci gaba da gudanar da irin wannan taron a gaba a kan al'amurran da suka shafi al'ummar Hausawa.