Ambaliyar Mokwa: Bago ya bukaci mazauna kogi da su ƙaura daga bakin gulabe

Ambaliyar Mokwa: Bago ya bukaci mazauna kogi da su ƙaura  daga bakin gulabe

Ambaliyar Mokwa: Bago ya bukaci mazauna kogi da su kaura, ya ba da gudummawar Naira Biliyan daya da filaye don sake tsugunar da wadanda abin ya shafa.

Daga Abbakar Aleeyu Anache. 

Gwamna Muhammad Umaru Bago na Jihar Neja ya yi kira ga mazauna yankunan koguna da ke fadin jihar da su gaggauta ficewa daga wadannan wurare masu rauni domin kare afkuwar asarar rayuka da dukiyoyi, sakamakon mummunar ambaliyar ruwa da ta afku a Mokwa.

Gwamna Bago ya dawo daga Saudiyya a ranar Lahadin da ta gabata ya ziyarci garin da ambaliyar ruwa ta shafa, ya kuma yi Allah wadai da wannan bala’in, yana mai bayyana lamarin a matsayin wani bala’i da jihar Neja ta fuskanta a wannan shekarar.

A wani nuna hadin kai, Gwamnan ya bayar da tallafin Naira biliyan daya domin tallafawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa. 

Ya kuma umurci ma’aikatar filaye ta Jiha da ta ware filaye mai yawa tare da bayar da takaddun shaidar zama ga Gwamnatin Tarayya don shirin sake tsugunar da mutanen da bala’in ya raba da muhallansu.