Sakkwato ta rasa wani babban mukami a gwamnatin Tarayya

Sakkwato ta rasa wani babban mukami a gwamnatin Tarayya

 

Shugaban kasa Bola Tinubu ya ya ba da sanarwar nada sabon  sakatare a hukumar tattara kudi  asusun 'yan sanda mukamin ya soma nan take.

Sabon sakataren Mista Mohammed Sheidu shugaban kasa na sanya ran zai yi amfani da kishin kasa da mutuncin da yake da shi wurin sadaukar da nauyin da ke saman kansa na samar da walwala ga dukkan 'yan sandan Nijeriya.
 Mai baiwa shugaban kasa shawara kan labarai da yadawa Ajuri Ngelale ne ya sanar da nadin, abin da ke nuni da cewa dan jihar Sakkwato da yake da rike da mukamin waton Abdullahi Bala ya sauka kenan har an maye madadinsa.