Abin fashewa ya kashe ɗalibi ɗaya da raunata huɗu a wata makaranta a Abuja

Abin fashewa ya kashe ɗalibi ɗaya da raunata huɗu a wata makaranta a Abuja

Wata mummunar fashewar bam ya faru a wata makaranta da ke wata unguwa a Abuja, inda ya kashe ɗalibi ɗaya kuma ya jikkata wasu huɗu, kamar yadda waɗanda suka ga abin da ya faru su ka shaida wa PREMIUM TIMES.

Wani jami’in tsaro ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:00 na rana a yau Litinin, a wata makarantar Islamiyya da ke unguwar Kuchibiyu, a yankin karamar hukumar Bwari, kimanin kilomita 42 daga tsakiyar birnin Abuja.

Wata majiya ta ce tawagar gaggawa da jami’an tsaro, ciki har da tawogar kwararrun jami'ai masu cire bam ta ƴansanda, sun isa wurin fashewar, yayin da aka garzaya da waɗanda suka ji rauni zuwa asibiti.

PREMIUM TIMES ta ce rundunar ƴan sanda ba ta saki wani bayani kan lamarin ba tukuna.