Ka San Babban Daraktan Aiyukka a Bankin Shigo Da Kaya Na Nijeriya

Ka San Babban Daraktan Aiyukka a Bankin Shigo Da Kaya Na Nijeriya

Daga Nabila Khamis

Shugaban kasa Bola Tinubu ya aminta da nadin Ibrahim Gaga a matsayin babban daraktan ayyuka a bankin shigo da kaya na Najeriya (NEXIM).

 
Mista Gaga, lauya ne wanda ya shafe sama da shekaru 25 yana harkar banki da ayyukan shari’a, a baya ya taba rike mukamin Sakataren Hukumar kuma mai ba da shawara kan harkokin shari’a a bankin NEXIM.
 
Ana sa ran nadin zai kawo sabbin himma ga aikin bankin NEXIM, a cewar mai magana da yawun shugaban kasar Ajuri Ngelale.
 
Ngelale ya ce Gaga zai mayar da hankali wajen samar da kudade, ayyukan rage kasada, bayanan kasuwanci da kasuwa, da kuma ayyukan ba da shawarwari na fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje da ke tallafawa manufofin bunkasa tattalin arzikin Najeriya.
 
Ya ce shugaban kasar na sa ran Gaga zai yi amfani da sabuwar rawar da ya taka wajen marawa gwamnatin shugaba Tinubu baya musamman a shirye-shiryenta na kawo sauyi.