What's Your Reaction?
Join our subscribers list to get the latest news, updates and special offers directly in your inbox
A jam'iyar PDP wadanda ake kallo sun hada da mataimakin gwamnan jihar Alhaji Manir Muhammad Dan'iya da Sakataren gwamnatin jiha Sa'idu Umar da Sanata mai wakiltar Sakkwato ta kudu Abdullahi Danbaba Dambuwa.
Sauran kuwa su ne Kwamishinan ma'aikatar ruwa ta jiha Umar Muhammad Bature da Alhaji Umar Ajiyan Isah da shugaban jam'iya na jiha Bello Goronyo.
A jam'iyar APC akwai tsohon mataimakin gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Ahmad Aliyu Sokoto da Ambasadan Nijeriya a Jordan Faruku Malami Yabo da Sanata mai wakiltar Sakkwato ta Gabas Ibrahim Abdullahi Gobir da Honarabul Abdullahi Balarabe Salame da tsohon ministan sufuri a Nijeriya Yusuf Suleiman da Sanata Abubakar Umar Gada da Dan Majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Gada da Goronyo a majalisar tarayyar Nijeriya Horabul Musa Sarkin Adar.
Shida daga cikin 'yan takarar sun fito daga Sakkwato ta Gabas hudu daga Sakkwato ta tsakiya uku daga Sakkwato ta Kudu.
A yankunan Sakkwato guda uku kowane yanki ya samar da Gwamna Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa daga Sakkwato ta gabas ya yi Gwamna daga 1999-2007, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko daga Sakkwato ta tsakiya ya karba daga 2007-2015, a yanzu kuma gwaman Aminu Waziri Tambuwal daga Sakkwato ta kudu ya fara daga 2015 har yanzu shi ne a kai.
Masu sharhi sun fahimci Alhaji Ahmad Aliyu da Ambasada Faruk Malami Yabo da Sanata Ibrahim Gobir a APC su ne suka fi karfi a cikin 'yan takarar gaba daya.
A hasashen masu nazarin siyasa da wuyar gaske dayansu ba shi ne zai yi wa jam'iyar takara ba domin za su iya samun goyon bayan jagoran jam'iyar APC a Sakkwato Sanata Aliyu Wamakko domin dukansu 'yan gidan siyasar ne.
Haka ma bayanin na nuna cewa sauran 'yan takarar a jam'iyar za su nemawa kansu magoya baya da kokarin samun damar takarar domin ba su da wani gidan siyasa a jihar, duk da wasunsu sun yi takarar a baya.
A PDP mataimakin gwamna da Sakataren gwamnati a gidan siyasar Tambuwal suke duk da ana kallon mataimakin gwamna ya raba kafa biyu hakan ya sanya ake ganin Jarman Sakkwato Alhaji Ummarun Kwabo zai iya goyon bayan takarar mataimakin gwamnan.
Wasu na ganin hakan zai sa Tambuwal ya goyi bayan takarar Kwamishinan Ruwa ko sakataren gwamnati ko shugaban jam'iyar PDP a jiha, dukkansu 'yan gaba ne a gwamnatin Tambuwal.
Sanata Danbuwa ana kallonsa tsohon dan siyasa ne da yake iya samun damar tsayawa takara a jam'iyar domin kusan shi ne kadai burin da ya tsayar da shi jam'iyar PDP yana da kuma sanayya ciki da wajen jihar Sakkwato duk ana yi masa kallon dan siyasar wayo.
managarciya Oct 30, 2021 12 169
managarciya Feb 3, 2025 3 110
Maryamah Dec 14, 2021 2 87
Maryamah Dec 16, 2021 10 73
managarciya Jun 24, 2023 5 73
managarciya Nov 13, 2023 0 550
managarciya Nov 12, 2023 0 346
managarciya Nov 12, 2023 0 335
managarciya Nov 12, 2023 0 416
managarciya Nov 11, 2023 1 702
managarciya Dec 8, 2025 0 24
managarciya Jan 29, 2025 0 113
managarciya Sep 11, 2021 1 709
Amma ya kamata uwaye su sani cewa,ba fa su kaɗai ne ke da hakki akan 'ya'yansu ba,...