Za mu karbi mulki hannu APC a 2023-----Tambuwal
Gwamnan jihar Sakkwato kuma shugaban kungiyar Gwamnonin PDP Aminu Waziri Tambuwal ya ce sun shirya sosai kan su a hade za su karbi mulkin Nijeriya a hannun jam'iya mai mulki ta APC da ikon Allah a 2023.
Tambuwal a wurin jawabinsa bayan kammala taron kungiyar Gwamnoninsu na tsawon awa 7 a gidan saukar da baki na gwamnatin Akwa Ibom ya ce "Muna tabbatar muku da ikon Allah a 2023 za mu gabatar muku da dakarun yaki cikin hadin kai da za su ceto Nijeriya daga mulkin rashin kwarewa na APC". a cewarsa.
Ya ce sun tattauna yanda jam'iyarsu za ta cigaba da zama kai a hade har bayan babban taron jam'iya hakan ne zai aika sako ga 'yan kasa cewa PDP ta shirya a matsayinta na dangi daya.
Tambuwal ya ce sun shirya a zaben jihar Anambra PDP ce za ta samu nasara da ikon Allah za su yi aiki tare domin samun nasara.