Ƙananan hukumomi 7 cikin 774 ne kacal ke da shafin yanar-gizo da ke aiki - ICPC
Ƙananan hukumomi 7 cikin 774 ne kacal ke da shafin yanar-gizo da ke aiki - ICPC
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da dangogin su, ICPC, ta baiyana cewa ƙananan hukumomi 7 cikin 774 da ake da su a fadin Nijeriya ke da shafin yanar-gizo da ke aiki yadda ya kamata, inda za a iya samun bayanai akan aiyukan su da kashe-kashen kuɗaɗen su da sauran bayanai masu muhimmanci.
ICPC ta ce rashin shafukan yanar gizon ga ƙananan hukumomi na haifar da nakasu wajen tabbatar da gaskiya da rikon amana wajen gudanar da shugabancin ƙananan hukumomin.
Musa Aliyu, shugaban ICPC na ƙasa ne ya baiyana hakan a wani shiri na Channels TV, Wanda tsohon hadimin mataimakin shugaban kasa, Laolu Akande ya gabatar a jiya Juma'a.
managarciya