An Ga Watan Azumin Ramadan A Nijeriya-----Sarkin Musulmi

An Ga Watan Azumin Ramadan A Nijeriya-----Sarkin Musulmi
Sarkin Musulmi ya ba da sanarwa ganin watan Ramadan a yau jumu'a ya ce sun samu labarin ganin wata daga shugabanni addinai da kungiyoyi daban daban a Nijeriya.
Hakan ke nuni da cewa watan sha'aban na shekarar 1443 ya kawo karshe, a gobe Assabar zata zama daya ga watan Ramadana a hijira 1443 dai da 2 ga watan Afirilun 2022.
Sarkin Musulmi ya bayyana cewa an ga watan ne a  wurare da dama 'mun aminta da sahihancin labarin ganin watan da aka yi a Sokoto  da Borno da katsina da  Filato da Kano da Kaduna da Zamfara da Yobe.
Ya roki musulmai su yaiwata addu'a acikin wannan watan  kan kawo karshen wannan annobar rashin tsaro da ta addabi Nijeriya .
Sarkin musulmi ya yi kira ga masu wadata su taimaki talakawa a watan Ramadana ba tare da kula da bambancin siyasa da kabila ba.
Sarkin musulmi bai zayyano garuruwan da aka ga watan ba, amma ya ce kwamitin ganin watan sun tantance sahihancin duk bayanin da aka samu kafin akawo maganar gaban shi.
 Sa kira ga shugabbani su kara kwarin guiwar ganin sun yaki matsalar tsaro da ake fama da ita a Nijeriya, a cigaba da yi wa kasa addu'a don samun cigabanta